1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Katar: Shiga tsakanin Hamas da Isra'ila

October 16, 2023

Muradun Katar da manufofinta ta fuskoki da dama da kuma gogewarta wajen shiga tsakani, sun sha gaban kusancinta da Iran da kuma Hamas a wannan rikicin da ake fama da shi yanzu.

https://p.dw.com/p/4Xaud
Zirin Gaza | Hamas | Isra'ila | Hare-Hare
Laluben hanyoyin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta FalasdinuHoto: Ariel Schali/AP Photo/picture alliance

Sakamakon kamarin yakin da ke wakana tsakanin Israila da Hamas, hankula sun fara karkata ga kokarin tattauna matakan tsagaita wuta da kuma yiwuwar musayar fursunoni. Zagayen farko na tattaunawar na kokari ne wajen yiwuwar musayar 'yan Israila 150 da wasu 'yan kasashen waje da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su, yayin da a hannu guda kuma za a saki Falasdinawa mata da yara kanana da ke tsare a gidajen yarin Israila. Kawo yanzu Masar wadda ta sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da Israila a 1979 da kuma ke da iyaka da Israila da yankin Zirin Gaza da kuma kasar Tukrkiyya da ke da dangantaka da Israila da kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da kuma Hamas, sun yi tayin shiga tsakani a rikicin.

Karin Bayani: Yakin Gabas ta Tsakiya ya dauki hankali

Katar da sau da dama a baya ta sha shiga tsakani kamar lokacin yakin Israila da Gaza a 2014, ta dawo domin sake shiga tsakani wajen samar da masalaha a tsakanin bangarorin biyu. Sai dai kuma duk da ta kawo karshen zaman tankiya da Israila a 2009, ta yi fice wajen taimakon kungiyar Hamas wadda kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Jamus da kuma wasu kasashe suka ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Daraktar Cibiyar Nazarin Al'amuran Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da ke da mazauni a London Sanam Vakil ta ce, a ganinta Katar ce ta fi dacewa ta shiga tsakani a wannan matsala tsakanin Israila da Hamas. Shi ma babban jami'i a Cibiyar Nazarin Tsaro da Al'amuran Kasa da Kasa da ke Berlin na Jamus kana mawallafin littatafai da dama a kan ta'addanci a Gabas ta Tsakiya Guido Steinberg na da ra'ayin cewa, Katar din ce ta dace da shiga tsakanin.

Ismail Haniyeh | Qatar | Doha | Hamas
Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh Hoto: Hamas Chief Office/ZUMA Pree Wire/picture alliance

Bugu da kari Katar ita ce ke kula da shelkwatar Hamas fiye da shekaru 10 da kuma shugaban Hamas din Ismail Haniyeh wanda ke zaune tsakanin Turkiyya da Doha tun shekarar 2017. A makon da ya gabata, Haniyeh ya fito tashar talabijin ta Aljazeera da gwamnatin Katar ke daukar nauyi, tare da bayyana matsayinsa kan harin da Hamas ta kai a Israila cikin alfahari ba tare da an yi masa wani sharhi ko martani ba. Cinzia Bianco ta Majalisar Kula da Dangantaka da Kasashen Ketare ta Tarayyar Turai, ta bayyana shakku kan cewa gwamnatin Katar ta san da harin tun farko ganin yadda ta rage bayar da kudi ga yankin Zirin Gaza tun ma gabanin harin ba-zatan da kungiyar Hamas din ta kai.

Karin Bayani: Isra'ila da Gaza sun kasa tsagaita wuta

A sakamakon haka a cewar Bianco hukumomin na Katar ba su da angizon da suke da shi a da wanda za su iya yin tasiri a yankin, haka ma kuma tashar AlJazeera ta Katar din duk da cewa tana da karfi amma tasirinta ya ragu ba kamar yadda ta ke ba kafin bullar kafofin sada zumunta na zamani ba. A waje guda 'yar uwar sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ta shiga shafukan sada zumuntar inda ta wallafa cewa yayin da fadar White House a Washington da kofar Brandenburg a Berlin da Opera na Sydney suka sanya fitilu launin tutar Israila domin nuna goyon baya, a nasu bangaren gidan adana kayan tarihi na Katar da gidan tarihin Musulumci a Doha an yi musu ado da tutar Falasdinawa. Sheikha  Al-Mayassa bint Hamad bin Khalifa al-Thani ta wallafa wadannan hotunan ne a shafinta na Instagram, tare da kalmomin larabci da ke cewa: "Ya Allah mun danka amanar Falasdinawa da al'umarta a hannunka."