1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laluben hanyar magance rikicin Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afarOctober 30, 2015

Manyan kasashen da ke fada aji a duniya sun amince da sake zama domin lalubo hanyar warware rikicin Siriya a siyasance.

https://p.dw.com/p/1GxS2
Taron tattaunawa domin kawo karshen rikicin Siriya
Taron tattaunawa domin kawo karshen rikicin SiriyaHoto: picture alliance/AP Images/B. Smialowski

Ministan harkokin kasashen ketare na Farsansa Laurent Fabius ne ya sanar da hakan ga manema labarai a wannan Jumma'a bayan kammala tattaunawar da suka yi a birin Vienna, inda ya ce sun tattauna batutuwa mafiya sarkakiya a kan rikicin na Siriya. Ko da yake ya ce akwai inda suka samu sabani sai dai sun samu ci gaba mai ma'ana kuma za su sake zama kan batun nan da makwanni biyu. Shima a nasa bangaren sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry ya ce akwai inda suka sha ban-ban da takwarorinsa na Rasha da Iran musamman kan batun ci gaba da mulkin Shugaba Bashar al-Assad na Siriyan. Kerry ya kara da cewa Amirka na da yakinin cewa saukar Assad daga kan karagar mulki ne kawai zai kawo karshen yakin da kasar ke fama da shi tare kuma da bayar da damar cin galaba a kan 'yan ta'addan IS da suka gallabi Siriyan, inda a hannu guda takwarorinsa na Rasha Sergei Lavrov da kuma na Iran Mohammad Javad Zarif suka nuna kin amincewarsu da saukar ta Assad, sai dai ya ce za su ci gaba da yin aiki tare. Wannan dai shine karo na farko da tattaunawa kan rikicin na Siriya ta hada dukkanin ministocin kassashen ketare na kasashen da ke da ruwa da tsaki a kan batun Yakin na Siriya.