1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090212 Griechenland Sparkpaket

February 10, 2012

Batun rage kuɗin fansho na ci gaba da raba kawunan shugabannin siyasar Girka

https://p.dw.com/p/140GY
Greek Finance Minister Evangelos Venizelos arrives for a meeting with Charles Dallara of the International Institute of Finance, a global bank lobbying group that is negotiating Greece's voluntary debt reduction, to discussed the writedown of debt in Athens, Monday, Dec. 12, 2011. Greece opened new talks in Athens Monday with international austerity inspectors on a second rescue loan package agreed weeks ago, but not yet finalized, intended to keep the debt-crippled country solvent while easing its crushing debt burden. (Foto:Thanassis Stavrakis/AP/dapd)
Ministan kuɗin Girka VenizelosHoto: dapd

Bayan tattaunawar tsawon sa'oi bakwai, ministan kula da harkokin kuɗi a ƙasar Girka Evangelos Venizelos ya garzaya zuwa birnin Brussels na ƙasar Beljiam domin bin sahun takwarorin aikin sa na ƙasashen Turai 17 dake yin amfani da takardar kuɗin Euro ta bai ɗaya a taron da suke yi, yana mai fatan samun nasarar ƙulla yarjejeniyar da za ta hana ƙasar sa faɗawa cikin kariyar tattalin arziƙi mafi muni, muddin dai ba ta sami kason kuɗi Euro miliyan dubu 130 da take buƙata nan da tsakiyar watan Maris ba. Sai dai kuma ministan ya nufi wurin taron ne, ba tare da cika ɗaukacin sharuɗɗan da sassa ukkun dake bada talafi, waɗanda suka haɗa da ƙungiyar tarayyar Turai da asusun bayar da lamuni a duniya IMF da kuma babban bankin tarayyar Turai suka gindaya ba.

Rage kuɗin fanso babbar matsala ce a Girka

Ko da shike firaminista Lucas Papandemos, tare da sauran shugabannin jam'iyyun dake ƙawance da jam'iyyar sa wajen gudanar da mulki a Girka, wato George Papandreau, da Antonis Samaras da kuma George Karatzerferis sun cimma yarjejeniya akan dukkan buƙatun tsuke bakin aljihun da suka haɗa da rage ma'aikata, da ƙara rage albashin ma'aikata, amma sun gaza samun daidaito akan batun neman tsimin kuɗin fansho na miliyan 300 da masu bayar da bashin suka gabatar musu. Hakan kuwa ya faru ne duk da cewar tattaunawar ta gudana ne tare da sanya idon wakilai daga tarayyar Turai da bankin Turai da kuma asusun na IMF. Sai dai wani ɗan Girkar ya ce babu alamar samun sauƙi a nan kusa: " Ya ce sannu a hankali dai sai ƙara tinƙarar mutuwa muke yi. Ta kowace fuska ka duba, komi ƙara taɓarɓarewa yake yi, babu inda mutum zai tsinƙayi wata kyakkyawar fata, sai dai kawai mutum ya ci gaba da fafutukar rayuwa ta yau da kullum

epa03093023 The leaders of the three political parties backing Lucas Papademos' (2 L) interim government -- PASOK leader and former prime minister George Papandreou (R), New Democracy (ND) leader Antonis Samaras (3 L) and Popular Orthodox Rally (LAOS) leader George Karatzaferis (L) are seen at the Maximos Mansion government headquarters during a critical meeting chaired by the Greek Premier to take the final decisions on the PSI and a second EU-IMF bailout loan to Greece, in Athens, Greece, 05 February 2012. EPA/ORESTIS PANAGIOTOU +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugabannin kawancen jam'iyyun dake mulki a GirkaHoto: picture-alliance/dpa

Yajin aikin gama gari a Girka

Babbar turjiyar da ake ci gaba da samu ga ƙarin matakan tsuke bakin aljihu a Girka, sakamakon kusan shekaru biyun da ma'aikata a ƙasar suka yi suna fama da rage musu albashi da kuma ƙarin haraji, baya ga tattalin arziƙin ƙasar dake cikin shekara ta biyar cikin matsala, kana da ƙaruwar adadin marasa aikin yi, sun tlastawa ƙungiyar ƙwadagon ƙasar kiran wani yajin aikin gama gari a ranakun Jumma'a da Asabar domin nuna adawa da ƙarin matakan tsuke bakin aljihun, abubuwan da kuma wani ɗan Girkar ya ce sai dai du'ai:" Ya ce Ta ko ina ka duba babu wani haske game da wannan masifar da muka faɗa ciki, kuma mutum bai san ma wanda zai dogara akan sa ba domin samun mafita. Muna dai ƙara fuskantar hatsari ne, wanda kawai ba'a bayyana shi a hukumance bane."

Demonstrators from the Communist-affiliated trade union PAME march to the parliament in protest against the new austerity measures in Athens February 7, 2012. Alarmed by the prospect of yet more budget cuts, Greece's two main trade unions hold a 24-hour strike on Tuesday in protest against policies they say have only driven the economy into a downward spiral. REUTERS/John Kolesidis (GREECE - Tags: POLITICS BUSINESS CIVIL UNREST EMPLOYMENT)
Boren adawa da matakan tsuke bakin aljihuHoto: Reuters

Mafita ga rikicin kuɗin Girka

Daga cikin mahalarta taron birnin Brussels da a yanzu Girka ke fatan za ta samu mafita dai, harda shugabar asusun bayar da lamuni a duniya Cristine Lagarde, da Mario Draghi, shugaban babban bankin Turai, yayin da a ƙasar Girkan kuwa ɗaya daga cikin shugabannin jam'iyyun dake ƙawance wajen jagorancin ƙasar George Karatzerferis ke cewar, nan da kwanaki ƙalilan suna fatan cimma matsaya akan ɗaukacin buƙatun masu baiwa ƙasar bashin.

Greek Finance Minister Evangelos Venizelos, center, looks at other ministers on a screen at his desk during a meeting of EU finance ministers in Brussels on Tuesday, Jan. 24, 2012. Greece's finance minister believes his country will be able to reach a deal with private bondholders to cut its debt, despite tougher terms set by its eurozone partners. (Foto:Virginia Mayo/AP/dapd)
Taron ministocin kuɗi na EuHoto: dapd

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmad Tijani Lawal