Neman warware rikicin Ukraine a siyasance
August 16, 2014Kamfanin dillancin labaran China na Xinhua da ya rawaito wannan labarin ya ce Shugaba Xi ya bukaci hakan ne loakcin da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ziyarce shi inda ya kara da cewar gaggauta samo bakin zaren warware mastalar zai taimaka wajen magance cigaba da dagulewar lamura tsakanin kasashen biyu.
Wannan kira na shugaban na China dai na zuwa ne daidai lokacin da kasahsen duniya ke cigaba da nuna fargaba ta sake fadadar rikici tsakanin kasashen biyu wanda hakan ka iya jawo karawa Rashan tsauraran takunkumi na karya tattalin arzki.
China dai na dasawa matuka da Rasha ta fuskar tattalin arziki domin ko a kwanakin da suka gabata bangarorin biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta cinikayyar isakar gas ta dalar Amirka miliyan dubu 400.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar