Neman wasannin olympics na shekara ta 2012 a birnin Leipizig
January 15, 2004Talla
Kowane daga cikin wadannan birane tara ya gabatar da bayani dalla-dalla a game da ikonsa na daukar nauyin wasannin Olympics da za a gudanar a bazarar shekara ta 2012. To sai dai kuma har yau da sauran rina a kaba. Domin kuwa takardun da aka gabatar sun kunshi amsoshin wasu muhimman tambayoyi ne guda 25 kacal da kwamitin Olympics ke neman bayani kansu.
Amma babu wani birnin da zai cimma nasarar daukar nauyin shirya wasannin na Olympics tare da amsa wadannan tambayoyi kawai. A yanzu ne aka bude babin takarar tsakanin illahirin biranen su tara dake fafutukar shirya wasannin a shekara ta 2012. Kuma a wannan marra da ake ciki ba wanda zai iya hasashen birnin da kwamitin zai ba wa fifiko. Wadannan birane zasu shiga takara har ya zuwa sha takwas ga watan mayu mai zuwa lokacin da kwamitin zai yi tankade da rairaya domin tace wadanda zasu shiga zagayen karshe na takarar. A tsakanin biranen da suka yi shaura ne za a zabi daya da ya cancanci daukar nauyin wasannin na shekara ta 2012 a Singapur a watan yuli na shekara mai zuwa. Tuni dai aka shiga yada jita-jitar cewa kwamitin na Olympics zai kayyade yawan ‚yan takarar zuwa birane shida a ranar ta sha takwas ga watan mayu mai zuwa.
Wato dai kwamitin zai tace birane uku ke nan daga cikin biranen guda tara. Amma fa shi kansa shugaban kwamitin ya sha nanata cewar mai yiwuwa ne fa dukkan biranen su samu nasarar tsallkawa zuwa zagayen karshe a watan yuli na shekara ta 2005, musamman idan dukkansu sun amsa tambayoyin da aka gabatar musu daidai, ba ragi, ba kari. Shi dai birnin Leipzig, ana iya cewar, ya tsallake rijiya da baya domin kaiwa wannan zagaye a daidai wa'adin da aka tsayar, ta la'akari da cece-kucen da aka sha famar fuskanta a game da birnin watan nuwamban da ya gabata. An fuskanci tabargaza iri-iri abin da ya hada har da ta kudi da sabani tsakanin kwamitin nema wa birnin wadannan wasanni, abin da ya kusa ya gurgunta ayyukan kwamitin baki daya.
Sabon shugaban da aka nada, Peter Zühlsdorff, wanda fitacce ne a matakan sabuntawa da farfado da ayyukan kamfanonin dake fuskantar barazanar fatara, shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen kare makomar wannan fafutuka ta nema wa birnin Leipzig damar daukar nauyin shirya wasannin na Olympics a shekara ta 2012. A dai halin da ake ciki birnin na Leipzig ya cika dukkan ka'idojin da kwamitin Olympics na duniya ya shimfida da yadda mai yiwuwa ya samu kafar tsallakawa domin shiga jerin biranen da zasu kai zagayen karshe na takarar neman nauyin shirya wasannin na Olympics da za a yi nan da shekaru takwas masu zuwa.
Talla