1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

060312 Netanjahu Obama Treffen

Usman ShehuMarch 6, 2012

Shugabannin ƙasashen Amirka da Isra'ila sun sanar da cewa baza su lamunta da shirin Iran na mallakar makaman nukiliya ba don haka sai inda karfinsu ya ƙare

https://p.dw.com/p/14FvS
President Barack Obama, right, meets with Prime Minister Benjamin Netanyahu, left, of Israel in the Oval Office at the White House in Washington, Friday, May 20, 2011. (AP Photo/Charles Dharapak)
Obama da Netanjahu a ganawarsuHoto: AP

Shugaba Barack Obama na Amurka da Firayimm ministan Isra'ila Benjamin Natenyahu sun bayyana cewar za su tsaya tsayin daka wajen ganin sun hana Iran mallakar makamin nukiliya. Cimma wannan matsaya dai ta biyo bayan wata ganawa da shugabannin biyu su ka yi a birnin Washington kan shirin nukiliyar Iran.

Shugabannin biyu dai sun ambata cewar za su yi bakin kokarinsu wajen ganin Iran ta dakatar da abin da su ka kira yunkurin mallakar makamin nukilya, wanda a cewarsu wata barazana ce ga zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Da ya ke jawabi kan wannan lamarin, firayim ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar duk da cewar an kakabawa Iran din tsattsauran takunkumin karya tattalin arziki, ko a jikinta, domin kuwa a cewarsa kawo wannan lokacin ba ta fasa ci gaba da abin da ya kira gudanar da bincike a shirin makamin nukilyar ba.

Iranian President Mahmoud Ahmadinejad gestures while speaking at the 25th International Islamic Unity Conference in Tehran February 8, 2012. REUTERS/Morteza Nikoubazl (IRAN - Tags: POLITICS RELIGION)
Iran Mahmud AhmadinedschadHoto: Reuters

A bisa wannan ne ma ya sa Netanyahun ya bayyana cewar dole ne Amurka da kasarsa su yi aiki kafada da kafada da juna wajen ganin sun dakile yunkurin Iran din na mallakar makamin na Nukilya.

Ya ce: "Ya zama wajibi a gare mu mu yi aiki tare domin kuwa tamkar danjuma da dan jummai mu ke"

Furta wadannan kalamai da Netanyahu ya yi dai sun biyo bayan irin goyon bayan da shugaba Obama ya ba wa Isra'ila inda ya ambata cewar zai baiwa kasar ta Bani Yahudu cikakken goyon baya dangane da shawo kan wannnan takaddama.

To sai dai duk da alwashin da aka ba Isra'ilan, firayim ministan na kasar ta Bani Yahudu ya bayyana cewar kasarsa za ta yi bakin kokarinta wajen ta kare al'ummar da ta ke mulka, domin kuwa ta na da cikakken ikon yin hakan.

Japan's ambassador to the International Atomic Energy Agency (IAEA) Yukiya Amano, seen prior to the start of the IAEA's 35-nation board meeting at Vienna's International Center, Monday, June 15, 2009. (AP Photo/Hans Punz)
Yukiya AmanoHoto: AP

"Idan ana batu na tsaron Isra'ila, to fa Isra'ilan na da cikakken ikon yanke shawara ta kashin kanta"

To amma duk da wannan, Firayim ministan ya ambata cewar za su bi hanya irin ta diplomasiyya wajen ganin sun cimma nasarar da su ka sanya a gaba wanda hakan ya yi daidai da irin matsayin da takwaransa na kasar Amurka wato shugaba Obama ya dauka inda ya ce daukar matakin diplomasiyya zai taimaka matuka gaya wajen fitar da kitse daga wuta.

"Mu na da yakinin cewar matakan diplomasiyya za su taimaka kan wannan lamari, dole su ma mahukuntan Iran su dauki irin wannan matsayi da za mu runguma domin a baya ba su yi hakan ba"

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum dai na ganin cewar shugaba Obama na wadannan kalamai ne a wani yunkuri na kauracewa amfani da karfi soji a kan kasar ta Iran.

(FILE) A file photo dated 20 August 2010 shows a general view of the nuclear power plant in Bushehr, south Iran, a day before the official opening ceremony. Iran's first nuclear reactor was connected to the national electricity network on 03 September 2011, Iran's Atomic Energy Organization said in a statement carried by ISNA news agency. The whole plant is to become fully operational on 12 September and to produce 1000 megwatts. EPA/ABEDIN TAHERKENAREH +++(c) dpa - Bildfunk+++
Atomkraftwerk Buschehr im IranHoto: picture alliance/dpa

To sai dai duk da wannan musayar yawun da ake ta yi kan shirin na Iran din game da mallakar makamin na nukiliya, Tehran ta bayana cewar ko alama shirin nukiliyarta ba shi da nasaba hada makamin kare dangi kamar dai yadda Isra'ila da Amurka ke ikirari.

Idan dai ba a manta ba, a 'yan makwannin da su ka gabata ne shugaban hukumar IAEA da mukarabbansa wadanda ke da alhakin bincike kan sha'anin makaman nukiliya su ka yi dirar mikiya a kasar ta Iran don gudanar da bincike sai dai shugaban hukumar Yukiyo Amano ya bayyana cewar ba za su iya tantance ko shirin makamashin nukilyar Iran din bai da nasaba da yunkurin mallakar makamin kare dangi ba.

Mawallafi: Klaus Kastan da Ahmed Salisu

Edita: Usman Shehu Usman