Isra'ila ta bukaci MDD ta canja wa dakarun UNIFIL matsuguni
October 13, 2024Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta sake tsugunar da rundunar kiyaye da zaman lafiya ta UNIFIL da ke aiki a kasar Lebanon a guri marar hadari. A cikin wani faifan bidiyo da aka watsa a ranar Lahadi an nuna mista Netanyahu yana gargadin Antonio Gurress kan cewa ya canja wa rundunar UNIFIL matsuguni ba ta tare da bata lokaci ba.
Karin bayani: MDD ta yi tir da harin Isra'ila a shalkwatar Lebanon
A daidai wannan lokaci Fafaroma Francis ya yi kira ga Isra'ila da ta mutunta wannan runduna wada hare-hare da ake zargin sojojin Isra'ilar sun kai da gangan a cikin sa'o'i 48 suka yi ajalin jami'anta akalla guda biyar a kudancin Lebanon.
Dama dai safiyar Lahadi wasu kasashe 40 da ke ba da gudummowa ga rundunar ta UNIFIL ciki har da kawayen Isra'ila sun fidda sanarwar bai daya inda suka ce ya zama dole a kawo karshen wannan aika-aika, sannan kuma sun bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.