Dan shekaru 37, Nicholas Opiyo lauya mai kare hakkin dan Adam ya tunkari kararraki masu tsauri a Uganda. Tare da yan tawagarsa, ya sami nasarar kalubalantar dokar adawa da luwadi sannan yak are sukar lamirin gwamnati da kuma wadanda aka ci zarafinsu. A 2017, Opiyo ya sami lambar yabo ta Jamus da Afirka game da kare hakkin bil Adama wanda lauyoyi kalilan ne ke sha'awar aiwatarwa.