Niger Delta: Jan kafa kan aikin gyaran muhalli
December 20, 2017Zanga-zangar ta wannan Laraba (20.12.2017) da wasu daga cikin al'ummar Ogonin suka gudanar ta hada da maza da mata da yara dama tsofaffi inda suka yi jerin gwano a kan titin Moscow Road wato harabar ofishin kamfanin man NNPC don baiyana kokensu. Zanga- zangar dai ba ta samu tsaiko ba ko kadan daga jami'an tsaro kuma wani abin lura babu wani jami'i daga kamfanin na NNPC da ya fito dan yi wa masu zanga-zangar jawabi.
Shekaru biyar da suka gabata, sashen kula da muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da kammala aikin tantance halin gurbacewar da yankin na Ogoni ya yi a sakamakon tsiyayar danyan mai na kamfanonin da ke aikin hakar suka yi tare da mika wa gwamnatin kasar sakamakon aikin tantancewar amma jan kafar da aka yi ta yi a gyaran muhallin ya haifar da cece-kuce musamman lokacin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daya fito daga yanki ya ke kuma jan ragamar kasar.
Gwamnatin Muhammadu Buhari a yanzu ta tabbatar da cewar za ta gudanar da aiki amman fa sannu a hankali za a yi shi don tabbatar da cewar an yi abin da ya kamata. Ga dukkan alamu hakan bai yi wa al'ummar dadi ba ganin matakin da suka dauka na sake yin kira ga gwamnati ta hanyar gudanar da zanga-zangar da kuma yin adawa da damar da aka bai wa kamfanoni aikin hakar mai ba tare da an cika musu alkawuran da aka daukar musu a baya ba.