SiyasaAfirka
Kammala janye sojojin Amurka daga Nijar
July 5, 2024Talla
A watan Afrilun wannan shekara ta 2024 ne dai, gwamnatin juyin mulkin sojan Nijar ta bukaci Amurka ta janye dakarunta daga kasar da ke yankin yammacin Afirka. Gabanin juyin mulkin watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2023 a Jamhuriyar ta Nijar da ya kawo karshen gwamnatin Mohamed Bazoum dai, kasar ta kasance mai dasawa da Amurka da ma sauran kasashen Yammacin Duniya. Sai dai tuni wannan alaka da ke tsakanin Nijar din da kasashen Yamma ta zama tarihi, inda mahukuntan sojan suka karkata zuwa Rasha.