1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An amince da sakamakon zabe a hukumace

Mahamane KantaMarch 8, 2016

Kotun kundin tsarin mulki a Nijar ta amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi makonnin da suka gabata, sai dai ba a kai ga fidda na 'yan majalisa ba don amincewa da shi.

https://p.dw.com/p/1I9ER
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Bayan shafe tsawon lokaci a na dakon bayyana sakamkon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Jamhuriyar Nijar, a cikin dare jiya hukumomi sun sanar da sakamakon a hukumance bayan da shugaban kasar da majalisar ministocinsa suka yi wani zama na musamman. To sai dai wannan sakamako da ka fidda bai kunshi sakamakon zaben na 'yan majalisar dokoki da aka yi rana guda ba.

Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hama Amadou da Shugaba Issoufou Mouhamadou za su fafata a zagaye na biyu na zabeHoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Da ranar wannan Talata din ce aka sanar da kunshin sakamakon. Wakilinmu da ke cikin 'yan jaridar da suka samu kwafi na wannan sakamako ya ce bai saba da sakamakon wucin gadi da hukumar zaben Nijar din ta CENI ta fidda kana ta gabatar a gaban kotun tsarin mulkin kasar. Bisa ga wadannan alkaluma da aka fidda a hukumance dai Shugaba Issoufou Mouhamadou na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki ne ke kan gaba da kashi 48 cikin 100 ya yin da Hama Amadou na jam'iyyar hamayya ta Moden Lumana Afirka ke da kashi 17 cikin 100.

Kasancewar babu dan takarar da ya samu kashi 50 ko fiye da haka cikin 100 na daukacin kuri'un da aka kada, yanzu haka za a je zageye na biyu na zaben kamar yadda aka bayyana tun da fari. Za kuma a yi wannan zageye na biyu na zaben ne tsakanin Shugaba Issoufou da Hama Amadou ranar 20 ga wannan watan na Maris da muke ciki. 'Yan adawa na Nijar din dai yanzu haka ba su kai ga cewa komai ba game da wannan batu sai dai sun ce da yammacin Talatar nan za su yi taron manema labarai domin fayyace matsayinsu kan lamarin.

Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Akwai yiwuwar 'yan adawa su yi watsi da wannan matsayi da aka dauka na amincewa da sakamakon zabenHoto: DW/M. Kanta