Nijar: An yi Jana'izar dalibai 27 da suka rasu a gobara
November 9, 2021An yi jana’izar ce karkashin jagorancin ministoci guda uku da shugaban kasa ya wakilto dauke da sakon ta’aziya da suka hada da ministan ilimi Dr Rabi’u Usman da ministan ma’adinai Madam Usaini Hadizatu Yakuba da kuma ministan cikin gida Alkashe Alhada tare da rakiyar gwamnan jihar Maradi malam Shaibu Bubakar da malamai da mai alfarma Sultan na Gobir da sauran manyan baki da al’umma gari.
Gawarwakin yara 27 mata goma sha biyar, maza goma sha biyu ne aka yi ma jana’iza kuma kowanne an gina masa kabarinsa daban. Alhaji Salissu agaji daya daga cikin wadanda suka yi ma yaran wanka da sutura ya ce bai taba ganin lamari mai tada hankali kamar wanan ba.
Bayan kammala jana’izar tawagar ministoci da shugaban kasa ya wakilto sun halarci taron addu’o’i a baban masalacin juma’a na fadar Sultan inda suka gana da iyayen yaran da suka rasu da yaran da suka jikata inda suka mika ta’aziyar shugaban kasa da ta gwamnati. An mika taimakon gaggawa na kudi cfa million ashirin ga iyayen wadannan bayin Allah.
Yanzu haka dai hankalin kowa ya koma kan makomar karatun yara kanana 'yan ajin reno da ajin shekarun farko na firamare .
Lawali Sabi’u shine mataimakin shugaban kungiyar iyayen dalibai ya ce ya kamata gwamnati ta kawo karshen amfani da dakunan makarantu na kara ko haki. A nata banagaren gwamnati ta dauki matakin hana amfani da dakunan karatu na kara ko haki
Masu yara kanana cikin makarantu sun shiga fargaba sai dai abin jira a gani shi ne cika alkawarin da aka dauka dan magance matsalar.