Bakin haure sun koma gida daga Libiya
July 20, 2019Akalla 'yan ci rani 900 ne 'yan asalin Jamhuriyar Nijar da ake rike da su a cibiyoyin rike bakin haure a kasar Libiya suka koma gida, daga farkon watan Janairun wannan shekarar zuwa yanzu kamar yadda wata majiya daga hukumar kula da kaurar jama'a ta MDD IOM ko OIM ta bayyana a yau din nan.
Ko a ranar Juma'ar nan wani jirgin shake da yan ci rani daga kasar ta Libiya ya sauka a birnin Niamey dauke da bakin haure 147 ciki har da wasu kananan yara tara.
Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa galibin wadanda aka dawo da sun daga Libiya 'yan asalin yakin Tahoua ne a yammacin kasar, da kuma na yankin Zinder da ke tsakiya maso kudanncin Jamhuriyar ta Nijar din wadanda dukkaninsu suka jima a hannun jami'ai da ke kula da cibiyoyin tare jama'a bakin haure da 'yan ci rani a kasar Libiya.