Nijar: Salou Djibo ya kalubalanci Bazoum
December 16, 2020Janar mai ritaya Salou Djibo wanda shi ma dan takara ne a karkashin jam'iyyar PJP Dubara ya sanar da shigar da kara a kan takarar Mohamed Bazoum a zaben shugaban kasa dangane da asilin sa na zama dan kasa. Salou Djibon wanda ya kira taron manema labarai a jiya ya ce ya shigar da kara a gaban kotu dangane da takardun Bazoum din na zama dan kasa wanda ya ce akwai bukatar kotu ta tantance. Wannan furci dai ya janyo wata sabuwar muhawara a Nijar inda aka yi la'akari da cewar tsohon shugaban kasar na mulkin soja Janar Salou Djibo wanda ya kifar da gwamnatn Mamadou Tanja a shekara ta 2010 shi ya bude kofa ga jam'iyyar PNDS tarayya wajan samun mulki. Tun da farko dai kotu ta yi watsi da karan jam'iyyar Modem Lumana Afrika ta Hama Amadou a kan batun takardun na zama dan kasa na Bazoum Mohamed.