Halitta da Muhalli
Matakan kare rakuman daji a Nijar
November 22, 2018Talla
A wani taron manema labarai da ya kira a jiya Laraba ministan muhalli na kasar ta Nijar Malam Almoustapha Garba ya ce sun dauki matakin ne domin kare lafiyar rakuman dajin na Koure wadanda ke zama garken karshe na nau'in irin wannan rakumin daji a duniya baki daya.
Ministan ya ce rakuman dajin wadanda guda 50 ne a shekara ta 1996 a fadamar ta koure, a yanzu sun kai 612 a yankin wanda sannu a hankali ke zama hadari ga rayuwar dabbobin a sakmakon yawansu da kuma yawan hadurran mota da mamayar hamada da sarar dajin da manoma ke yi don samun filin noma.
Matakin kwashe wasu rakuman dajin na Koure zuwa Gadabedji inda da ma rakuman suka yi rayuwa a shekarun baya zai shafi a tashin farko rakuman 10 maza uku.