1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kididiga game da mulkin Tiani daga kungiyoyi

Salissou Boukari AH
November 1, 2024

Kungiyar M62 ta gabatar da sakamakon jin ra'ayin jama'a wanda a cikinsa 'yan kasar suka yi magana kan abubuwan da suke so da ma wadanda suke neman a daidaita sahu a kansu.

https://p.dw.com/p/4mV5W
Hoto: CNSP

  Babban abu na farko dai dan ya fito a cewar shugaban wannan kungiya ta M62 da ta aiwatar da binciken jin ra’ayin jama’a a jihohi takwas na kasar ta Nijar shi ne na daukan mataki na hukumomin na Nijar suka yin a korar duk wasu barakokin soja da ke cikin kasar da aka girka ba bisa ka’ida ba da kuma yunkurin samar wa kasa cikeken 'yancin inda ake kokarin ganin arzikin kasa ya zaman ana 'yan kasa. Falamata Moctar Taya daya daga cikiin manyan kusoshin kungiyar ta yi tsokaci kan al’amuran da suka fi dauka musu hankali dangane da sakamakon da suka samu na jin ra’ayin jama’a inda ta ce bayyanan sun gamsar da su.

Niger Protest gegen die US-Militärpräsenz in Niamey
Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

A fannin abubuwan da binciken ya nunar danganeda ra’ayoyin 'yan kasar ta Nijar da aka jiyo kann tafiyar mulkin na sojoji a wannan lokaci, kashi sama da tamanin sun ba da ra’ayoyinsu na cewa lokaci bai yi ba yanzu na mika wa 'yan siyasa mulki domin a baya an nunar musu cewa mulkin demokaradiyya tamkar dama ce ga 'yan siyasa su yi abun da suka ga dama ba tare da bin dokoki na ita demokaradiyyar ba kaman yadda Falmata ta ci gaba da yin bayani:Sai dai da yake sharhi kan sakamakon binciken bayan da da suka tattara alkaluma, shugaban wannan kungiya ta M62 Abdoulaye Saidou, ya ce an lura cewa akasari wasu na amfani da jahilcin al’umma ne wajen cusa musu ra’ayoyi na kyamar shugabannin da ke da niya kokarin fidda kasa daga mugun kangi kaman lokacin marigayi Baare Mainassara, Tanja Mamadou da dai sauransu inda ake fifita kuskuran da suka yi a kan aikin kwarai duk kuwa da cewa dan Adam mai laifi ne, inda ya ce su kuma 'yan siyasa sun yi amfani da jahilci da talauci na al’umma, inda cin hanci da rashawa gami da arzuta kai da dukiyar kasa ya zamana tamkar shi ne tubali na mulkin da suke yi, lamarin da ya haddasa kyama da tsana ta 'yan siyasa a zukatan al’umma bayan zuwan mulkin   soja.