1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Cece-kuce da UNDP kan binciken tsaro

Gazali Abdou Tasawa
August 13, 2024

A Jamhuriyar Nijar sabon cece-kuce ya taso kan matakin hukumomin mulkin sojan kasar na haramta wa hukumar UNDP bincike kan yanayin tsaro da ta kuduri aniyar gudanarwa a kasar.

https://p.dw.com/p/4jOcR
Niger | General Tchiani übernimmt Macht nach Putsch gegen Präsident Bazoum
Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

A yayin da wasu ‘yan kasar ke ganin hukumar ta UNDP na da wata manufa ta dabam da ta ke son cimma a binciken na ta, wasu na ganin gwamnatin sojin ba ta son ‘yan kasa da duniya su san irin barnar da Nijar ta fuskanta a fannin tsaro a tsawon shekara daya na mulkinsu. 

A cikin wani sako da ministan cikin gida ya aika wa gwamnonin jihohi bakwai na Nijar da kuma na birnin Yamai, ya sanar da su cewa ya samu labarin hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya wato PNUD ko kuma UNDP ta soma gudanar da wani bita da kuma auna girman matsalar tsaro a fadin kasar Nijar. Ministan cikin gidan ya ce wannan bincike haramtacce ne dan haka ya umurce su da su dauki duk matakan da suka dace domin hana hukumar ta PNUD gudanar da wannan aiki. Ma'aikatar cikin gidan kasar ta Nijar ba ta bayar da wasu dalilai na daukar wannan mataki ba. Sai dai tuni wasu daga cikin masu goyon bayan mulkin sojan irin su Malama Falmata Taya ta kungiyar M62 ta ce sun fahimci matakin magabatan nasu wanda ta ce yana a kan turba 

Wasu sojojin kasar Nijar a bakin aiki
Wasu sojojin kasar Nijar a bakin aikiHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

"Wannan mataki da aka dauka kan hukumar raya kasa maganinta kenan. Saboda munaficin da suka saba yi a Nijar shi ne suka zo su yi yanzu. Kowa ya sani a Nijar kudi suke bayarwa a yi zabe. Ko da lafiya ko babu, ko akwai tsaro ko babu su ba abin da ya sha masu kai. Su abin da ke damunsu a gudanar da zabe a yi yadda suke so, su kuma su zo su ci gaba da cin karensu babu babbaka. Sannan hatta 'yan ta'addan da ke damun mu su da kansu ne Turawan da ke cikin irin wadannan kungiyoyi suke basu kudi su basu makamai don su zo su yake mu dan saboda arzikin ma'adananmu saboda arzikinmu. To wanda suke sa wa suna yi mana ingiza mai kantu ruwa su yi abin da suke so, to babu shi yanzu"

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da dama masu adawa da mulkin sojan Nijar ke zargin sa da boye wa ‘yan kasar alkaluman koma bayan da Nijar ta fuskanta a fannin tsaro a shekara daya ta mulkin soja da rahoton UNDP din ka iya bankadowa.

Wasu sojin NIjar sun kwanta dama a harin 'yan ta'adda
Wasu sojin NIjar sun kwanta dama a harin 'yan ta'addaHoto: Boureima Hama/Getty Images

Abin jira a gani a nan gaba shi ne ko gwamnatin kasar ta Nijar da hukumar ta UNDP za su tunkari juna domin samun fahimtar juna a nan gaba kan batun wannan bincike wanda ke daga cikin ayyukan da hukumar Majalisar Dinkin Duniya ke aiki da su wajen fitar da tartibin kasashen duniya a fannin ci gaban kasa da ta rayuwar dan Adam a kowace shekara. Alkalumman da a baya rashinsu ya sa  suka sa hukumar ke dora Nijar a matsayin kasa ta kutal a duniya