Nijar: Cece-kuce kan rufe kamfanin Cominak
October 28, 2021Tun dai bayan da aka sanar da rufe kamfanin na COMINAK babban kamfanin hakar karfen Uranium na jamhuriyar Nijar bisa dalillai na rashin cinikin karfen Uranium a kasuwannin duniya tun bayan hadarin kasar Japan na Fukushima a shekara ta 2011. Nijar ce kasa ta hudu a duniya daga cikin jerin kasashen da ake fitar da wannan karfe na Uranium wanda batun rufe kamfanin ke a matsayin hanya mafi dacewa a cewar ministar kula da ma’adinai ta Jamhuriyar Nijar Madame Ousseini Hadizatou Yacouba, wadda ta ce daman shi kamfani ana kafa shine domin a ci riba.
Shi dai wannan kamfani na COMINAK wanda a yanzu aka rufe kofofinsa, an kafa shi ne sama da shekaru 40 inda aka yi ta tono da karfen na Uranium a kasar ta Nijar, Sai dai kuma tun lokacin rufewar da ya zo a cewar minista Madame Ousseini Hadizatou Yacouba, gwamnati ya kafa kwamiti daban-daban tare da daukar kwararru don ganin an yi komai cikin tsanaki ta yadda ba za a samu wani babban cikas ba a fannin gurbatar muhalli ko kiwon lafiyar al'umma..
Sai dai daga nasu bangare 'yan kungiyar farara hula masu bin diddigin wannan lamari sau da kafa musamman ma a garin Arlit inda kamfanin yake ta bakin Almoustapha Alhassan, lalle sun ji dadin da minista ta fito domin bada ba’asi, amma kuma ya kyautu a sani cewa su ba wai suna ganin laifin gwamnatin Nijar ba ne suna ganin laifin kamfanin ORANO na kasar Faransa ne domin gwamnatin Nijar ta bashi wuka da nama wajen hakar ma’adinain na Uranium.
Baya dai ga wannan babban kamfani na hakar Uranium da aka rufe na COMINAK, akwai kamfanin SOMAIR da shi yake aiki a yanzu, kuma a cewar Ministar ta ma’adinai ta jamhuriyar Nijar, sannu a hankali nan zuwa yan shekaru masu zuwa, bukatun Uranium zasu kara tasowa, inda ma wasu da a baya suka karbi takardar izini suka soma tunanin girka nasu kamfuna domin hakar karfen na uranium sannan kuma gwamnatin ta Nijar ta bada damar tsoffin ma’aikata da ke da sani kan lamarin su kasance a sahun gaba ko da wani sabon kanfani zai zo a nan gaba.