Mahamane Ousmane yayi fatali da kame kamen yan adawa
February 28, 2021Talla
Mahamane Ousmane da ya ayyana kansa a matsayin wanda yayi nasarar zaben shugaban kasa zagaye na biyu, ya yi fatali da barazanar da yace ake ci gaba da yiwa magoya bayan jam'iyyun adawa, tun bayan barkewar tarzomar bayan zabe da ta yi sanadiyar mutuwar mutun biyu a birnin Yamai.
Ya zuwa yanzu dai ana dakon kotun tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu, wanda hukumar zaben CENI ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasararsa da kaso 55,75% , sakamakon da madugun adwar Mahamane Ousmane ke ci gaba da karyatawa,