Nijar: Gabatar da kungiyoyin farar hula a kotu
May 17, 2018Shugabannin kungiyoyin farar hular wandanda aka zargin dai sun hada da Nouhou Arzika, da Ali Idrissa, da Moussa Tchangari sai kuma fitaccen lauyan nan mai zaman kansa Maitre Lirwana Abdourahamane da dai sauransu.
Sanye da riga da wando na yadin zube mai launin ruwan kwai da fari da babbar hula Maitre Lirwannna Abdourahmane na daya daga cikin jiga jigan kungiyoyin farar hullar nan na hudu da hukumomin Nijar suka kargame yau sama da kwanaki 50 da suka bayyana a yau a gaban alkali a karon farko tun bayan zanga zangar nan da hukumomin Nijar suka haramta da kuma aka gudanar a ranar 25 ga watan Maris da ya gabata.
Maitre Lirawana na tafe ne da rakiyar wasu mutane guda hudu ciki har da ma’iakacin wata kungiyar mai zaman kanta ta kasa da kasa IRD da suka gudanar da yajin aiki na cin abinci a kwanakin baya bayan nan a gidan yarin Dai Kaina da ke yankin Tillabery. Wannan dai shi ne karon farko da alkali ke sauraren dan farar hular, kuma lauya mai zaman kansa da zummar samun bahasi da cikakken bayanin abin da da ya wakana a ranar ta zanga-zangar 25 da watan Maris.
Maitre Mahamane Rabiou daya ne daga cikin lauyoyin da ke kare 'yan farar hullar, ya ce ya zuwa yanzu duk wata tuhumar da ake yi wa wadnda suke karewa bata da tushe. "Shi fa laifin nan da ake zarginsu ba wani laifi ba ne, saboda laifi ne da aka jima ana samun irin wanna shari’ar. Kenan idan an lura kawai akwai wani lauje ne cikin nadi kai ko bisa yakin 'yan ta’adda ta kamata a girmama doka. Gashi an kama mutane an hana hakkin jama’a don shi ne muke ta kalubalantar kamun su muna cewar ya sabawa ka’ida".
Yin da yake fira da DW Malam Nayoussa Djimraou, babban sakataren kungiyoyin farar hula na MPCR ta Nouhou Arzika, ya ce matsin lambar da suka yi shi ne ya tilasta wa alkali sauraren jiga-jigan kungiyoyin. "Ba a so a fara sauraren mutanenmu ba, yanzu tilas ne ta kama garesu don su soma shi. Kuma lauyoyinmu kada ku manta sun kalubalanci alkalin da ya soma sauraren shari’ar, to kawo yanzu alhamdulillah muna fatar a yi shari’ar domin mun san abukanmu ba su da laifi. Mafi yawansu daga wuraren da aka kama su basu da laifi, kowa yana shirye don tunkarar shari’a"
Duk da cigaba da rike abukanen tafiyarsu fiye da 25, kungiyoyin fararen hullar sun ce ba za su yi sanyi a gwiwa ba, face sai sun tilasta wa gwamnatin tankwasowa daga matsayinta na tsayin gwamnin jaki kan dokar ta kasafin kudi, wace suka kira mai cike da cece kuce.
Gwamnatin dai na cigaba da nacewa kan matsayinta na cewar babu wata babbar illa ga dokar da 'yan farar hullar suke kalubalanta, saboda hakan babu wata alama ta tsayawa da su domin tattaunawa. A wannan Jumma'a ake sa ran rukunin karshe na 'yan kungiyoyin farar hular da aka kama za su bayyana a gaban kotu don samun yin tozali da alkali, lamarin da bangarori da dama a kasar ke jiran ganin yadda zai kaya.