An sulhunta daliban jami'a da gwamnatin Nijar
May 15, 2018Bangarorin biyu sun cimma daidaito ne biyo bayan takun saka da ya kai ga gwamnati daukar matakan rufe ilahirin wuraren kwanan dalibai a jami'oi daban daban, sai dai duk da haka gwamnatin Nijar ta ce za ta ci gaba da daukan matakan tsaftace jami’o’in kasar daga bata gari da daliban bugi.
Dalibai da dama sun yi fari cikin cimma matsayar sai dai haryanzu jami'an tsaro na jibge a harabar jami’ar birnin Yamai, tun bayan barkewar kazamar zanga-zangar dalibai da ya yi sanadiyar rufe wuraren kwanan na tsawon makonni uku. Ministan Ilimi mai zurfi Malam Yahouza Sadissou Madobi, ya bayyana dalilan suka suka ja hankalin gwamnati sake bude wuraren.
Yace " Dalili na farko shi ne kungiyar dalibbai ta dage yajin aikin karatu, kenan wajibi gwamnati ta bude gidajen kwana da gidajen cin abinci da sauransu. Kuma tuni kusan ko ina dalibai sun koma karatu in banda jami’ar Tahoua da Zinder."
Matsalar rufe dakunan kwanan daliban ya shafi akalla dalibai dubu 20 a jami’ar Abdou Mumini da ke birnin Yamai, amma kakakin kungiyar daliban jami’ar Abdou Moumouni Tsalha Kaila, ya ce ba su gindaya wa gwamnati sharuda ba kamin sake bude dakunan kwanan daliban.
Yace " Dole ne domin ba zata yiwu ba kace mutun yaje karatu kuma babu wurin kwanciya, babu wurin cin abinci. Kenan dole ne a bude kuma idan har ba a biya mana sauran bukatun ba,muna iya amfani da matakanmu, kuma muna iya fitowa ta inda ba su yi tsammani ba."
Hukumomin ilimin mai zurfi a Nijar sun bayyana anniyarsu ta cigaba da tsaftace makarantun jami’o’in kasar, "Domin samun damar kula da tarbiyar su, don gudun kar bata gari su lalata tarbiyarsu" inji ministan ilimi mai zurfi Malam Yahouza. Kimanin Jami’o’in Nijar Takwas ne ke ta bore sakamakon neman wasu hakkokinsu, amma gwamnati ta sha cewa tana yunkurin sharemusu hawaye.