Za ayi zaben kananan hukumomin Nijar
July 25, 2020Talla
A karon farko hukumar zaben Jamhuriyar ta Nijar CENI, ta mayar da cikeken martani kan zargin da 'yan adawa suka yi mata, na hada baki da masu mulkin kasar domin tabka magudi a yayin manyan zabukan da ke tafe.
Tun da fari dai hukumar zaben ta Nijar wato CENI, ta bayyana ranar 13 ga watan Disamban da ke tafe a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda mafi yawan jam'iyyun siyasa har ma da na adawa suka bukata.