1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar jam'iyyar MNSD Nasara na cikin ruɗani

Abdourahamane HassaneNovember 5, 2014

Jam'iyyar ta tsohon shugaban ƙasar Nijar Tanja Mamadou ta kori wasu ƙusoshinta guda 35.

https://p.dw.com/p/1Di2v
Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Alhaji Saini Oumarou shugaban jam'iyyar ta MNSD NasaraHoto: DW/M. Kanta

Daga cikin waɗanda jam'iyyar ta kora har'da Abouba Albade,ministan ƙasa,wanda shi ne babban sakataran jam'iyyar,da Alma Oumarou ministan kasuwanci,shugaban jam'iyyar reshen Zinder.

Tun farko jam'iyyar ta ce ta kori waɗannan 'yan siyasa amma daga bisani suka shigar da ƙara kotu ta soke korar. Jam'iyyar ta fara samun rarabuwar kawuna ne tun bayan da wasu ya'yan jam'iyyar suka shiga cikin gwamnatin haɗin kan ƙasa.