An kada gangar siyasa a Nijar
February 8, 2021Da farko dan takarar adawa ne Mahamane Ousmane ya kaddama da yakin neman zaben a Jihar Tillabery da ke a yammacin Njar. A jawabin da ya gabatar a wajen wannan taro dan takarar adawa Alhaji Mahaman Ousmane ya bayyana daurin kansa a game da yadda matsalar tsaro ke kara kamari a Nijar tare da shan alwashin kawo karshen wannan matsala idan an zabe shi.
Dan takarar adawa Mahamane Ousmane ya kaddamar da kampe din sa shi ma a Tillabery
Yayin da a yau kuma dan takarar jam'iyyar da ke mulki ta PNDS taraya Bazoum Mohamed ya kaddamar da yakin neman zabensa a Jihar ta Tillabery. Madugun ‘yan adawqar Nijar Malam Hama Amdou wanda ke da karfin fada a ji a cikin Jihar ta Tillabery ya yi kira ga al’ummar yankin da ta yi watsi da duk wata akida ta kabilanci ko bangaranci da wasu ‘yan siyasa ke yadawa domin kishin kasar nan ta hanyar jefa wa Mahaman Ousmane kuri’a. a zaben mai zuwa