1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen tsaro da tsadar rayuwa a lokacin azumi a Nijar

Issoufou Mamane MNA
April 12, 2021

A yayin da al'ummar Musulman duniya ke tunkarar azumin watan Ramadan, a jamhuriyar Nijar al'ummar kasar ne ke fuskantar kalubale iri-iri da suka hada da na tsaro da na annobar corona har ma da na tsadar rayuwa.

https://p.dw.com/p/3rtpj
'Yan sanda na sintiri a birnin Yamai a jajiberen fara azumin shekarar 2020
'Yan sanda na sintiri a birnin Yamai a jajiberen fara azumin shekarar 2020Hoto: NICOLAS REMENE/AFP/Getty Images

A cikin 'yan shekarun baya bayan nan dai kasar ta Nijar na cin karo da jerin matsaloli ciki kuwa har da na yawan hare-hare da ke jefa al'ummar yankuna da dama cikin fargaba, hadi da matsalar annobar COVID-19 da ta jagule al'amura da dama, yayin da farashin cimaka ke dada hauhawa, abin da ke zaman wani babban nauyi ga kasar kamar yadda Alhaji Nuhu Magaji wani mai nazarin al'amuran yau da kullum ke cewa.

"Hare-haren da wasu kungiyoyin na 'yan ta'adda ke kawowa cikin kasa, wannan abu ne wanda ya kamata su jami'an tsaro da gwamnati su zage dantse wajan ganin shi wannan abu su taka mishi birki, domin akwai kalubale na cutar COVID, akwai kuma hare-hare akwai kuma matsaloli na zabe wanda aka yi da kasar ta fuskanta. Wato wadannan abubuwa sun yi wa Nijar yawa, sun yi nauyi. Idan ma ta kama a yi wani zama na tsaro ko kuma a tattara wasu kungiyoyin wadanda ke da karfin fada a ji a cikin kasa, wadanne hanyoyi ne ya kamata a bi wajan tunkarar wadannan matsalolin da suka dabaibaye Nijar. Ita tsadar rayuwa idan aka ce kasa ba ta sarrafa abubuwa na masarufi daga kayanta na noma to wannan shi ne ummal uba'isar wasu abubuwan na tsadar rayuwa da ke zuwa, to mu muka jawa kanmu.''

Musulmi na yawaita yin ibada da addu'o'i a lokacin azumin watan Ramadan
Musulmi na yawaita yin ibada da addu'o'i a lokacin azumin watan RamadanHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

A cikin wannan yanayin ne na tsaro da fargaba da zaman dar-dar da na kalubalen tsadar rayuwa, al'ummar musulman kasar za su fadawa cikin kwanaki 30 na watan azumin Ramadan duk da cewar dai a shekarar bana an samu sassaucin dokokin cutar COVID-19,  wadanda a bara suka tauye jama'a ciki ma har da rashin sallar tarawi a masallatai.

Karin bayani: WHO: Za a samu karuwar corona a watan azumi

Sai dai ga tallakawan kasar akwai bukatar amfani da wannan watan domin neman sauki daga Indallah a cewar Basiru Boda wani magidacin.

"Lokaci ne wanda ya zo a daidai wasu abubuwa wadanda kamar Allah kawai ne za a roka. Wannan watan da haka za a iya, ban da rokon Allah shi kawo sauki babu abin da za a yi.

Tsadar rayuwa, matsalar tsaro, duk saï da dan gari a kan ci gari, duk abin da ke faruwa mune ke janyo shi."

Abincin buda baki irin su kunu da kosai sun fi samun karbuwa a kasar Hausa
Abincin buda baki irin su kunu da kosai sun fi samun karbuwa a kasar HausaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Maikatanga

Duk da dai ana cikin wannan yanayin an samu wasu kungiyoyin agaji da ke taimaka wa jama'a musamman marasa karfi kamar su marayu da uwayensu ta hanyar ba su daukin cimaka, hatsi, shinkafa, man girki, suga da sauransu, domin su fuskanci wannan watan mai alfarma a cikin tsanaki.

Alhaji Abdulmumuni, mamba a kwamitin wata kungiyar agaji, yayiwa tashar DW karin bayani

''Marayu sun fi kowa shiga cikin matsala saboda wadanda ke kula da su Allah ya karbi rayuwarsu, ga talauci ya yi yawa."

Jama'a dai na tattare da fatan ganin an samu wata kafa daga gwamnati ta saka yawunta wajan rage tsadar rayuwa a watan azumin na bana.