1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kisan fararen hula a Inatas ya janyo cece-kuce

September 7, 2020

A jamhuriyar Nijar muhawara ta barke akan kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi wa jama'a fararen hula a garin Inatas da ke jihar Tilaberi bayan da hukumar kare hakkin bil Adama ta CNDH ta bankado batun.

https://p.dw.com/p/3i7yP
Niger Armee | Opfer nach Angriff
Hoto: DW/S. Boukari

Garin Inatas yana kan iyaka ne da kasar Mali inda ke da matsalar tsaro, bayan yan fashi da makamai da kuma rikici tsakanin al'umma a waje guda kuma ga 'yan ta'adda da masu ikrarin jihadi wadanda suka yi dandazo a yankin. 

A lokuta da dama dai idan aka sami matsalar tsaro ko yaki ana kashe mutanen da basu ji basu gani ba.

Dan majalisa dokoki Sa'adu Dillena jam'iyyar PNDS tarayya da ke mulki yace kafin aukuwar wannan lamari an sha kai hare hare da ke salwantar da rayukan dakarun tsaro a yankin.

Duk da mutuwar wadannan jama'a fararen hula wasu manazarta na ganin babu wani sauyi da za a samu a game da sha'anin tsaro da kuma aikin da sojoji ke yi a yankin