1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin gano bakin zaren warware matsalolin ilimi a Nijar

September 6, 2018

Kwararru kan ilimin karatun boko a fadin Nijar na musayar yawu a taronsu na shekara-shekara karo na 5 a Damagaram, domin nazarin matsalolin ilimi ko akasin haka.

https://p.dw.com/p/34ReV
Schule in Niamey
Hoto: DW/A. Mamane Amadou

Kyakyawan jagoranci cikin tafiyar ilimin karatun boko dai shi ne taken taron na bana da ke zaman na biyar a tarihi. Kwararru kan ilimin karatun boko a fadin kasar ta Nijar ke musayar yawu a taron na shekara-shekara da birnin Damagaram ke daukar bakoncinsa.

Maman Sanussi Sabro ministan ilimin makarantun boko shi ne ya jagorancin bude taron da a ciki za a duba batun burin da gwamnatin kasar ta sa gaba na kai matakin cimma kaso daga 60 cikin 100 a matakin sakandare zuwa kaso 55 cikin 100 a matakin gaba da sakandare kafin shekara ta 2021.

A shekarar da ta gabata dai sakamakon karshen shekara a matakin shahadar BEPC ya tashi da kaso 39.61 cikin 100, yayin da a bangaren BAC aka samu kaso 25.75 cikin 100, matsalar da a cewar minista Sanussi Sabro an samu cikas a dakokin kasa wadanda suka shafi wannan fanni.

Schule in Niamey
Hoto: DW/A. Mamane Amadou

"Ana samun wadanda ke bin son ransu ba sa aiki da dokokin kasa a fannin ilimi. Sai ka tarar yara ba sa zuwa makaranta amma ba a daukar wani mataki na ganin sun je makaranta. Shi ke sa ana samun yara ba sa cin jarrabawa da kyau. Amma yanzu mun dau matakai na yin gyara."

Saley Elhaji Labo mai kula da alkalumma ne daga hukumar ilimin makarantun boko mai zurfi, a nasu gani alkalumman na bana sun fi na bara kyawo duba da irin chakulkulon da karatun bokon ya fuskanta duk da ma sahihan alkalumman adadin yaran da aka kora an lullubesu.

Taron yana kuma mayar da hankali ga batun daukar matakin bayar da horo ga malamai da kuma bi sau da kafa na duk wasu masu hannu a cikin tafiyar ilimi, kama daga iyaye zuwa malamai.
Taron dai ya zo daidai da takun sakar da ya tilasta kwararrun malaman jami'o'in kasar yajin aiki na mako guda inda a hannu daya kuma ya rage makwanni biyu kacal sauran dalibai su koma bakin azuzuwansu a fadin kasar.