Shawo kan matsalar tsaro a Nijar
May 6, 2021Shugaba Mohamed Bazoum ya kwashe dogon lokaci yana tattaunawa a fadarsa da Janar Marc Conruyt babban kwamandan na rundunar Barkhane ta sojojin Faransa da ke yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel.
Karin Bayani: Kokarin tabbatar da tsaro a wasu kasashen Sahel
Ayayin ganawar tasu, babban kwamandan rundunar ta Barkhane ya bayyana wa manema labarai cewa sun tattauna ne kan matsalar tsaro a yankin Sahel baki daya da kuma hare-haren da Nijar ta fuskanta a baya-bayan nan, inda sojojinta da dama suka halaka. Tuni dai al'ummar Jamhuriyar ta Nijar suka soma tofa albarkacin bakinsu kan wannan ganawa da kuma fa'ida ko akasi na zaman sojojin kasashen ketare a Nijar da ma yankin Sahel baki daya.
Da yake jawabi ga manema labarai, babban kwamnadan na rundunar ta Barkhane ya ce ya kawowa Shugaba Bazoum ziyara ne ta kashin kansa, koda yake wasu na ganin kalamai ne na diplomasiya inda suke ganin cewa shugaban Nijar din ne ya gayyato shi domin ya bayar da bahasi kan yanayin tsaron. Yanzu haka dai al'ummar ta Nijar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan fa'idar wannan ganawa tsakanin Shugaba Bazoum da shugaban rundunar ta Barkhane.
Karin Bayani: Mafita ga yankin Sahel da Tafkin Chadi
Babban kwamnadan rundunar ta Barkhane ya ce sojojin rundunar tasu da na G5 Sahel da kuma na kasashen yankin, na samun nasara akai-akai a fagen daga, amma kuma turjiya da 'yan ta'addan ke ci gaba da nunawa, na nuna bukatar sojojin kasashen su kara zage damtse a yakin nasu da kungiyoyin 'yan ta'addan.