Nijar: Lamura na ci gaba da gudana sannu a hankali
August 18, 2023A yayin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta saka wa Nijar jerin takunkumai na tattalin arziki bayan juyin mulkin da ya wakana, lamura na ci gaba da gudana sannu a hankali inda mai karamin karfi ke kara kasancewa cikin mawuyacin halin rayuwa musamman a wannan lokaci na damina inda sabon amfanin gona bai kai ga fitowa ba.
Sai dai a cewar Mamane Nouri na kungiyar ADDC Wadata, har yanzu farashin na nan gidan jiya. Shima Issa Bori Abbas wani mai sayar da hatsi ya ce farashin hatsin da masara ya dada hawa.
Magidanta dai masu saye domin amfanin gida su ma sun koka da tsadar kamar yadda Alhaji Maman Sani wani magidancin ya bayana.
Tun bayan da aka sanar da takunkumin kungiyar ECOWAS kan kasar Nijar, kasashen Mali da Burkina Faso suka ce ba za su yi biyayya ga wannan umarni na ECOWAS ba inda suka ce iyakokinsu za su ci gaba da kasancewa a bude sai dai a cewar Mamane Nouri hakan lallai zai kasance mafita amma sai an samar da tsaro. Abin jira a gani dai shi ne yadda lamuran za su kance zuwa gaba idan ba a samu sasantawa tsakanin kasashen na ECOWAS da sabbin hukumomin na Nijar da suka yi juyin mulkin ba.