Nijar: Martani kan ziyarar shugaban Areva
February 20, 2017Ziyara ta mukaddashin kamfanin na Areva Philippe Varin a garin Arlit cikin dare ta jawo cece-kuce sosai musamman ma ga mazauna garin da kuma kungiyoyin fararen hula a jihar Agadez, inda yanzu haka su ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta. Guda daga cikin fitattun 'yan kungiyoyin fararen hula a Arlit Almoustapha Alhassan ya shaida wa wakiliyar DW a Agadez cewar wannan ziyara ta Mr. Varin na da ayar tambaya musamman ma da ya ke cikin dare ya yi ta. Talakawan na jihar Agadez ma dai ba a barsu a baya ba wajen tofa albarkacin bakunansu kan wannan ziyara, inda da dama ke cewar kamfanin ya shafe shekaru 40 ya na tonon Uranium a Agadez amma ya zuwa yanzu ba su gani a kasa ba.
Sanusi Mahaman da ke zaman guda daga cikin 'yan jihar cewa ya yi ya kyautu hukumomin jihar Agadez da ma shugabannin kananan hukumomi su fito don yi wa al'umma bayani kan wannan ziyara da mukaddashin shugaban na Areva ya kai yankin na Arlit, da nufin tantance makasudin zuwan nasa. Kungiyoyin fararen hula a jihar Agadez dai yanzu haka na ci gaba da Allah wadai da irin kawancen da Nijar ke da shi da kamfanin Areva, inda suka bayyana cewar ba a yin abin da ya dace wajen aikin tonon karfen Uranium kana suna fatan nan gaba shugabannin su gyatta yadda tafiyar ke gudana kana a rika yi wa al'umma bayani game da yadda lamura ke wakana idan ana batu na tonon ma'adanin na Uranium, wanda ke jibge a karkashin kasa a jihar ta Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar.