1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mo Ibrahim: Martani kan karrama shugaban Nijar

Gazali Abdou Tasawa MNA
March 9, 2021

A Jamhuriyar Nijar masu fafutikar kare dimukuradiyya sun mayar da martani kan kyautar Mo Ibrahim ta wannan shekara da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya samu.

https://p.dw.com/p/3qP3C
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Hoto: AFP/I Sanogo

Shugaban kasar ta Nijar, Mahamadou Issoufou, ya samu wannan kyauta ce da ke karrama shugaban da ya nuna tafiyar da mulki na gari da ci gaban kasarsa, bayan da aka share shekaru hudu ba tare da kwamitin bayar da kyautar ya bai wa wani shugaba ita ba a bisa hujjar cewa babu wanda ya cancanta a ba shi ita.

Karin bayani Wannan dai shi ne karo na bakwai tun bayan kafa gidauniyar ta Mo Ibrahim da ke bayar da wannan kyauta wacce shugabanni irin su Ellen Johnson Sirleaf ta Laberiya da ma Nelson Mandela na Afirka ta Kudu suka taba samu. Shugaban kasar ta Nijar Mahamadou Issoufou ya samu kyautar ta gidauniyar Mo Ibrahim ta bana a sakamakon a cewar gidauniyar iya shugabanci da raya dimukuradiyya da kuma samar da ci gaba a kasarsa. Malam Foumakoy Gado shugaban fadar shugaban kasa ya ce kyautar da shugaban kasa ya samu abin alfahari ce ga Nijar baki daya.

Mo Ibrahim attajirin kasar Sudan da ya kafa gidauniyar karrama shugabanni na gari a Afirka
Mo Ibrahim attajirin kasar Sudan da ya kafa gidauniyar karrama shugabanni na gari a AfirkaHoto: DW/F. Quenum

To sai dai Alhaji Idi Abdou na kawancen kungiyoyin farar hula na Rotab kana dan fafutikar dimukuradiyya a Nijar ya ce kyautar da aka bai wa shugaban kasar ta Nijar ta zo masu da mamaki domin a ganinsa bai cancanci ya same ta ba.

To sai dai a daidai lokacin da wasu masu fafutikar kare dimukuradiyya ke cewa shugaba Issoufou bai cancanci samun wannan kyauta ta Mo Ibrahim ba, wasunsu na ganin babu ma wani mamaki a cikin lamarin ta la'akari da ayyukan da shugaban ya yi a shekaru 10 na mulkinsa. Malam Samna Inoussa na kawancen kungiyoyin farar hula na Convergeance citoyenne pour la demokratie et la Rep na daga cikin masu irin wannan ra'ayi.

Wannan kyauta ta Mo Ibrahim dai ta tanadi bai wa wanda ya lashe ta, kudi tsaba har Dalar Amirka miliyan biyar a cikin shekaru 10 masu zuwa.