Nijar: Martanin MNSD ga sabuwar jam'iyyar MPR
October 12, 2015A Jamhuriyar Nijer 'yan awoyi kalilan bayan bangaren Alhaji Albade Abouba wanda ya jima yana jayayya a jam’iyyar adawa ta MNSD ya kafa tasa jam’iyyar biyo bayan kayin da ya sha a gaban kotu, babbar jam’iyyar ta adawa ta ce Allah raka taki gona ga tsoffin 'yan twayenta, amma ta ce kofofinta a bude su ke domin sake karbar tsaffin bijirarrin 'ya'yan nata idan suka amince da su yi nadama.
A yayin wata firar da yayi da tashar DW hausa ne dai mataimakin shugaban jam’iyyar adawar ta MNSD Nasara kuma jigo a reshenta na jihar Maradi Alhaji Ali Sabo ya nuna gamsuwa da matakin da bangaren na Albade Abouba ya dauka na kafa tasa jam’iyyarsa bayan shafe tsawon shekaru biyu ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu wanda da kyar da sudin goshi kotu ta kai ga yanke hukumcin. Mataimakin shugaban jam’iyyar dai ya zargin bangaren Albade Abuba da taka wata muhimmiyar rawa wajan tsarin wargaza jam’iyyar ta adawa domin kurum abin da ya kira barin Shugaban kasa Issoufou Mahamadou shi kadai ya samu damar kai labari a zaben shugabancin kasa da za’a yi a farko farkon watan Febrarun sabuwar shekara.
MNSD ta ce Allah raka taki gona da kafa jam'iyyar MPR
" Duk wannan kokowar da ka gani wannan abin da aka ma MNSD Nasara, zamansu na tsutsa cikin goro da suka ma mu wannan kokowar da aka sa su yi, Mahamadu Isufu ya saka su yi ta. Yanzu kamar gona ce idan ka fidda mata tsambare bunkasuwa take. Na tafiya sun tafi wannan ko dimun akwai rasuwa akwai haihuwa cikin duniya kuma mun san yau abin da aka sakasu a ciki don su wargaza Nijar ne mun sani, don Isufu ya samu wa’adi na biyu ne tunda da sun fito da dan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa da mun masu kirari mun ce diya ne "
A nasu bangare kwa kusoshin jam’iyyar ta MPR Jamhuriya cewa suka yi duk wasu kalaman suka ko rudani tsakanin bangarorin biyu nasu da na jam’iyyar MNSD mai adawa sun riga sun kare, babban abin da ke a gaban sabuwar jam’iyyar shi ne na kafata tare da bata sabuwar alkibla. Alhaji Ibro Ayouba kakakin jam’iyyar MPR jamhuriya ne mai jagorancin Albade Abouba.
Jam'iyyar MPR ta mayar da hankali ga aikin kafuwarta a cikin kasa
" Tsakaninsu da mu yanzu sai dai hulda ta jam’iyya da jam’iyya irin wadda za mu yi da ko wace jam’iyya. In kana jayayya ne da mutun za ka samu ya gaya maka wata magana ko ka gaya mashi. Amma yanzu mu gabanmu aikin mai yawa ne ko da yake tsoffin tutoci ne za’a janyewa a saka sabbi kawai"
A yayin wani taron manema labarai da madugun 'yan adawar kasar ya kira kuma Shugaban jam’iyyar ta Mnsd mai cikakken 'yanci a yanzu Alhaji Seini Oumarou ya tabo batun tsoffin magoya bayan nasu da cewar kofofin MNSD na bude ga duk wadanda suke bukatar dawowa idan sun gano da cewar sun fada kuskure.
Seini Oumarou ya yi tayin kome ga tsaffin 'yan tawayen jam'iyyarsa
"Gaskiya ne halin da tsoffin abukanin tafiyarmu suka nunawa jam’iyyar ya yi muni sosai to amma sai dai kamar yadda muke fadi ne da cewar duk wadanda suka ga suna da niyyar dawowa da zuciya daya idan har suka gano da cewar an yi masu wani dabo ne to muna tarbonsu da hannu biyu biyu domin gina jam’iyya"
Sai dai batun dawowar gida da madugun 'yan adawar ke yi wa tsaffin abukanin tafiyar sun kasance tarihi in ji kakakin jam’iyyar MPR jamhuriya ta Albade Abouba Alhaji Ibro Ayouba.
" Wannan sai dai a saka shi cikin tarihi domin babu wata dama a ce a yi wata gyara. Tare ne ake, za’a zauna tare da za’a yi duk wani abin da zai samu na alkhairi"
A tsakiyar watan Agustan shekara ta 2013 ne dai rikici ya barke a cikin wasu manyan jam’iyyun siyasa sakamakon anniyar shugaban kasa ta kafa wata gwamnatin hadin kan kasa wacce ta bar baya da kura a cikin manyan jam’iyyun siyasar da suka jima suna kai ruwa rana a kotu. Cikin wadanda suka fada wanan matsalar har da babbar jam’iyyar adawa ta MNSD, Jam’iyyar da shugabanta ya ce ko ta halin kaka za su kalubalanci shugaban kasa a zaben farko na shugabancin kasa da za’a yi a cikin watan febraru na sabuwar shekara