1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar: Muhimmancin sarakunan gargajiya wajen inganta tsaro

January 18, 2024

Sarakunan Gargajiya na da muhimmiyar rawar takawa cikin al'amuran zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar cikin kasa baki daya.

https://p.dw.com/p/4bPyq
Hoto: Salissou Kaka/DW

A kan haka ne haka ne wata kungiyar kasa da kasa (Stars group consulting Niger) tare da goyon bayan gwamnati suka shirya wani kasaitaccen taro na wayar da kan sarakunan Gargajiya na jihar Maradi kan muhimancin zaman lafiya da kishin kasa.

Bayan jihar Agadez da Zinder da kuma Diffa tawagar kungiyar kasa da kasa ta Stars group consulting ta kawo rangadi a birnin Maradi inda ta gana da galibin sarakunan gargajiyan domin waye musu kai kan kishi da sanin mutuncin kasa a cikin tafarkin zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'uma.

Tawagar mai dauke da sako na musamman daga shugaban kasa zuwa ga uwayen kasa na neman su cigaba kamar yadda suka saba wurin jan hanlin al'umominsu, na su tashi tsaye tsayin daka wurin gudanar da ayukan cigaban kasa. Lokaci yayi na daina duk  wani tashin hankali tare da nuna kishin kasa shi ne tubali na gina kasa.

A cikin takaitaccen jawabinshi mai martaba sultan din Katsinar Maradi Ahmed Ali Zaki ya ce abun da ya kamata ga 'yan kasa shi ne, a kara hada kai an zama tsintsiya madaurinki guda an nuna kishin kasa kuma anyi aiyukan gina kasa.

Sarakunan gargajiya suna bakin kokarinsu wurin wayar da kan al'umominsu sai dai suna bukatar a basu matsayinsu kuma a kama musu cewar mai martaba Mansur Kane Mai Gizo sarkin Tasawa.

Tawagar zata isa Tahoua da Dosso da Tillaberi kafin ta karkare zagayen da birnin Yamai a wata mai kamawa.