1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Boren kin jinin sojan Faransa ya barke a yammacin Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
November 27, 2021

Bayan da aka tare su har na tsawon kwanaki a Burkina Faso, tawagar sojan Faransar da ke kan hanyar zuwa Mali ta gamu da turjiya a garin Tera mai nisan kilomita 200 da birnin Yamai.

https://p.dw.com/p/43Zuj
Frankreich Mali - Militär Konflikte
Hoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Akalla mutane uku ne suka rasu wasu 18 kuma suka jikkata a yayin masu adawa da sojojin Faransa suka tare ayarin sojan da ke kan hanyarsu ta zuwa Mali. Sai dai jami'an tsaron Nijar, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harbin gargadi ta sama, a yunkurin da 'yan zanga-zangar suka yi na farwa wasu daga cikin motocin a cewar kakakain jami'an tsaro. Tuni dai rahotanni suka ce ayarin sojan ya bar yankin na Terra a wannan yammaci. Sai dai wannan boren na zuwa a yayin da ko a jiya shugaban kasar Mohamed Bazoum a wani jawabinsa ga 'yan kasar, ya nuna gamsuwa da aikin sojan na Faransa, da ma irin yadda huldarsu ta ke tafiya ta fannin yaki da ta'addanaci.