Nijar na ci-gaba da kawar da azuzuwan zana
June 27, 2023Gobara da ke wakana a azuzuwan zana a wasu makarantun bokon Jamhuriyar Nijar ta yi sanadiyyar mutuwar dalibai da dama a 2021. Saboda haka ne shugaba kasa Mohamed Bazoum ya sha alwashin kawo karshen amfani da azuzuwan zana sama da 30,000 da ke da akwai a fadin kasar. Tuni ma gwamnatin kasar ta kaddamar da aikin soma gina sabbin azuzuwan na siminti wadanda suka soma samun goyon baya daga kasashe da kungiyoyi masu hannu da shuni da ma Bankin Duniya. Ko da Idi Harouna, jami'in kula da shirin maye gurbin azuzuwan zana zuwa na siminti a Nijar, sai da ya ce shirin ya samu tallafi na Bankin Duniya.
Makarantu kwana na 'yan mata za su wadata
Baya ga gina azuzuwan zamani, tallafin Bankin Duniya zai taimaka wajen gina makarantun kwana na 'yan mata domin bunkasa ilimin 'ya'ya mata a kasar Nijar. Sai dai shugaban kungiyar COAD Amadou Roufa'i Lawal Sallaou ya yi kira ga gwamnatin NIjar da ta kula wajen bayar da kwangilar gina azuzuwan na zamani. Shi kuwa Nayoussa Jimraou da ke zama malamin makaranta a Nijar cewa ya yi samar da azuzuwan zamani zai taimaka wajen inganta yanayin karatu da kauce wa haduran gobara da ke neman zaman ruwan dare a makarantun bokokn kasar.
Baya ga Bankin Duniya , Bankin Raya Kasashen Afirka ta Yamma na BOAD ya dauki nauyin gina wasu azuzuwan zamanin guda 1000, a yayin da wasu kungiyoyin na kasa da kasa da masu hannu da shuni suka dauki nauyin gina makarantun kwana na 'yan mata a kasar ta Nijar.