1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na fuskantar dambarwar siyasa

April 23, 2014

An shiga kwanaki na biyar a rikicin siyasar da ya dabaibaye ayukan yan Majalisun Jamhuriyar Nijar, sakamakon zaben membobin Zartaswa.

https://p.dw.com/p/1BnaG
Hajiya Hauwa Abdu
Hoto: DW/Mahamman Kanta

A jamhuriyar Niger a wannan Laraba ce (23.04.2014) aka shiga kwana na biyar a ci gaban da ake kan wata danbarwa da ta taso tsakanin yan Majalisun dokokin kasar na bangaran masu rinjaye da takwarorinsu na adawa, a game da batun girka sabon kwamitin zartarwa na Majalisar.

Matsalar dai ta samo tushe ne bayan da wasu yan Majalissar dokoki na rukunin yan adawa dake marawa gwamnati baya su ka ki amincewa da takarar wani daga cikin takwarorin nasu, a bisa hujjar cewa ba a shawarce su ba wajan bada sunasa, inda akayi ta tayar da jijiyoyin wuya a zauran Majalisar dokokin.

Musabbabin Rikicin:

Da farko dai yan Majalisun sun yi nasarar zaben membobin kwamitin kolin guda 10 daga cikin 12 ba tare da wata matsala ba,to amma daga bisani rikicin ya taso ne a lokacin da aka zo zaben mataimakan shugaban Majalisar dokoki na biyu da na ukku wadanda gurabe ne biyu da doka ta baiwa yan adawa su.

Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW
Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Wasu yan Majalisun na bangaran adawa da suke marawa bengaren masu rinjaye baya, sunyi watsi da takarar Honorable Falke Basharu akan mukamin mataimaki na biyu na shugaban Majalisar da rukunin yan Majalisun na ARN, wanda ya hada jam'iyun MNSD Nasara, CDS Rahama, da kuma UNI ya gabatar. Honorable Seidu Ama na daga cikin yan Majalisar da a halin yanzu suke marawa bengaran masu rinjaye baya suka yi watsi da dan takarar da kawancan na ARN ya gabatar da sunan bengaran yan adawa.

Rukunin mu na mutun talatin ne, to amma mutun 14 su ka tafi su ka yi taro, su ka tsaida abun da suke so ba tare da halartar mu mutun 16 ba, su kace ba za su yarda mus higa taron ba, mu kuma muka ce muddin muna cikin wannan rukuni, to kuwa mun wuce inda wani zai je ya yi wani abu da sunan mu ba tare da ya gaya mana ba, mu kuma muka ce tun da ba su yarda da mu ba, mu kuma ba za mu amince da wanda za su tsaida a matsayin dan takara ba.

Rukunin yan Majalisun dokokin kawancan na adawar na ARN dai, ya yi nasarar hana zaben dan takarar da abokanen nasu masu tawaye suka gabatar, duk kuwa da cewa sun samu goyan bayan illahirin yan Majalisar na bangaran masu rinjaye, abun da kuma bangaran kawancan na ARN din da ke goyan bayan takarar Honorable Falke Basharu, suka danganta shi da cewa rashin adalci ne.

An nuna rashin adalci da rashin sanin ya kamata, kan mutanan da muka tsaida da sunan mu yan adawa, a ce an ki kama masu alhali su yan bangaran masu rinjaye da su ka yi mun tsaya tsakani da Allah mun kama masu, to amma abun mamaki da aka kawo ga namu sai su ka ce suna goyan bayan wadanda su aka yi mana tawaye, kwana biyar ko shidda yau mun tsaida aiki sabo da wannan batu, tun da sun fi son wadannan masu goyan bayansu da Niger gaba daya, to mu dai yan adawa mun yi tir da Allah wadai da wanan abun.

Bengarori na zargin juna

Yan Majalisar dokoki na bangaran adawa dai, sun zargin takwarorinsu na banagaran masu rinjaye da yin katsalandan cikin harkokinsu, ta hanyar marawa wadanda su ka kira yan tawayensu baya. To sai dai da ya ke mayar da martani akan wanann zargi dan Majalisa Asumana Malam Isa na jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki cewa ya yi yan adawar ba su ta fadi ne kawai...

Yau dama mutun in ya rasa ta fadi, sai yayi ta kame kame, domin wadannan mutanan duk lokacin da ake karbar kudi na tarbace na tafiyar da aiki ana karbar kudadansu amma in ya kasance za'ayi wata shawara, ba a kiransu, su ka zo su ka ce mu maramasu baya, to mu kuma ba 'yan cin amana ba ne tun da wadannan mutane kowa ya gani da rana tsaka, su ka fito su ka ce su suna goyan bayan shugaban kasa, sun yarda da aikin da ya ke yi to kenan har gobe in mutanan nan suka kawo kukan su za mu goya masu baya in kuma zabe za a yi a Majalisa duk abun da su ka nema za mu kama masu.

A yau ma dai jim kadan bayan buda zaman taron Majalisar aka dage shi har ya zuwa yamma, a sakamakon ci gaban sabanin da ake samu tsakanin yan Majalisun dokokin. Sai dai kuma a daidai loakcin da wanann dambarwa ta ki ci ta ki cinyewa a Majalissar dokokin a hannu daya kuma an gudanar da taron hukumar sasanta rigingimun siyasa na CNDP wanda ya tantamna batun kidayar yan kasar ta Niger mazauna kasashen ketare da za su shiga zabuka masu zuwa dama akan batun yin aiki da sabon rijistan zabe na zamani a zabukan masu zuwa.

Mawallafi: Boukari/Gazali Abdou
Edita : Umaru Aliyu