SiyasaAfirka
Nijar na shagulgulan karamar sallah
May 1, 2022Talla
A Jamhuriyar Nijar a wannan Lahadi ne al'ummar Musulmin kasar ke gudanar da shagulgulan karamar sallah ko sallar azumi ta bana. Gwamnatin kasar ta bayar da umurnin gudanar da sallar a wannan rana bayan da hukumar koli ta harkokin addinin Muslunci ta kasar, Conseil islamique, ta sanar da ganin jinjirin watan Shawal a garuruwa akalla biyar na kasar a yammacin ranar Asabar.
Wakilin DW a Yamai Gazali Abdou Tasawa ya ce '' kusan gaba daya Musulimin kasar suka yi bikin sallar a wannan Lahadi.''
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar sun halarci sallar Idin a Yamai, suna masu isar da sako na zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.