1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rikici ya barke a tsakanin dalibai da hukumomi

Abdoulaye Mamane Amadou
April 18, 2018

Hukumomin ilimi mai zurfi sun dauki matakin rufe wurin kwanciyar daliban jami’ar Yamai bayan wata hatsaniyar da ta barke tsakanin daliban jami'ar da jami’an tsaro a bisa korar wasu daliban da aka yi.

https://p.dw.com/p/2wI38
Niger Niamey Studentenproteste
Hoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Ministan Ilimi mai zurfi Malam Yahouza Sadissou ya tabbatar da daukar matakin, inda ya ce lamarin ne ya yi kamari duba da yadda aka farfasa motoci da kuma lalata ginin hukumar da ke a jami'ar ta Yamai.

Da sanyin safiyar yau ne dai daliban suka soma wani gangami a harabar jami’ar da zummar nuna bacin ransu kan korar wasu daga cikin jiga jigan kungiyar daliban jami’ar ta UENUN biyar, gangamin da kuma daga bisani ya rikide zuwa rikici. 

Duk da ya ke an rufe wuraren kwanciyar daliban, gwamnatin ta ce za a ci gaba da karatu. Ba tun yau ba daliban jami’ar kasar ke ta takun saka da gwamnati sakamakon fitowar da suke yi akai akai don neman ganin gwamnatin ta inganta rayuwarsu, a bara a ranar 10 ga watan Afrilu, wata zanga zangar daliban jami’ar ta Yamai ta yi sanadiyar mutuwar dalibin nan mai suna Malah Bagale Kelemi.