1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta gabatar da jadawalin zabe

Gazali Abdu Tasawa/ ZMAJuly 30, 2015

Shugaban hukumar zaben kasar ta CENI mai shari'a Ibrahim Boube ne ya bayyana lokutan da za a gudanar da zabukan shekara ta 2016 mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1G7af
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

A jamhuriyar Nijar hukumar zaben kasar wato CENI ta bayyana jadawalin zabukan da kasar ke shirin gudanarwa a farkon shekara mai kamawa. Jadawalin ya tanadi shirya zaben shugaban kasa a jimilce da na 'yan Majalissar Dokoki a ran 21 ga watan Febrarun shekara ta 2016; Zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a ranar 20 ga watan Maris 2016, kana zaben kananan hukumomi a ranar tara ga watan Mayu na shekarar ta 2016.

Shugaban hukumar zaben kasar ta Nijar mai shari'a Ibrahim Boube ne ya bayyana hakan lokacin wani taron manema labarai da ya kira inda ya bayyana cewa jadawalin ya samu amincewar illahirin mambobin hukumar ta CENI a wani zama da ta gudanar a ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata. Tuni dai hukumar zaben ta mika wa gwamnatin kasar wannan jadawali.

Sai dai 'yan adawar kasar ta Nijar na nuna shakkunsu a game da adalcin Kotun Tsarin Milkin kasar wacce za ta tantance mutanan da suka cancanci tsayawa takarar a zabukan masu zuwa.

A saurari sautin rahoto daga wakilimmu na Yamai Mahamman Kanta, a kan jadawalin zaben.