Nijar ta jaddada ci gaba da rufe iyakarta da Benin
May 12, 2024Firaministan Nijar ya jaddada cewa iyakar kasar da Benin za ta ci gaba da kasancewa a rufe saboda dalilai na tsaro, sai dai amma ya ce da akwai yuwar samar da mafita kan dambarwar fitar da danyen man kasar ta tashar jiragen ruwa ta Seme Kpodji da ke Jamhuriyar Benin din.
Karin bayani: Rikici tsakanin Nijar da Jamhuriyar Benin
A yayin wani taron manema labarai da ya yi a jiya Asabar a birnin Yamai, firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce Nijar ta yanke wannan shawara ne saboda akwai sansanonin sojin Faransa a Benin, kuma ya yi zargin cewa a wasu daga cikin wadannan sansanoni Faransar na bai wa 'yan ta'adda horo domin su kawo hargitsi a Nijar din.
Firaministan ya ambato wasu gurare biyar a Benin inda ya ce a can ne Faransar ka horar da masu gwagwarmaya da makamai kamar yadda ta yi a baya a wani yanki da ake wa lakabi da Park W wanda ke kan iyakar Nijar da Burkina Faso.
Ali Mahaman Lamine Zeine ya kuma kara da cewa Nijar za ta kasance cikin shiri domin sake bude iyakarta da Benin da zaran ta tabbatar da cewa barazana ta tsaro ta kawa.
Karin bayani: Fitar da man Nijar ta Benin cikin gagari
A game da batun fitar da man fetun din Nijar ta tashar jiragen ruwa ta Seme kuwa Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce yana fatan za a samu mafita tare da ba da tabbacin cewa fadar mulki ta Yamai ta bukaci bangaren China da ya tattauna da mahukuntan kasar ta Benin.