1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sojan Nijar sun hallaka 'yan Boko Haram

Abdoulaye Mamane Amadou
May 26, 2022

Dakarun Jamhuriyar Nijar sun yi ikirarin halaka mayakan Boko Haram 40 a wasu tsibirai na yankin Tafkin Chadi a yayin da suka yi nasarar dakile yunkurin wani mummunan hari.

https://p.dw.com/p/4BszY
Symbolbild | Nigeria | SWAT
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/Planetpix/A. F. E. Lii

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma'aikatar tsaron kasar ta kara da cewa, dakarunta sun yi nasarar kwace makamai da dama daga hannun 'yan ta'addan. Sai dai bakwai daga cikin sojojin Jamhiriyar ta Nijar sun ji rauni sakamakon taka nakiya da motarsu ta yi, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.

Wannan dai ba shi ne farmaki na farko da dakarun hadin gwiwa da ke yaki da ta'addaci suka kai a Tafkin Chadi ba. Ko a farkon wannan watan na Mayu, rundunar kasashen Chadi Kamaru Nijar da Najeriya da ke yaki da Boko Haram FMM a takaice, ta kaddamar da wani samame kan mabuyar 'yan Boko Haram a yankin inda ta halaka mayaka kimanin 20.