1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta samu sabuwar gwamnati mai membobi 38

Salissou BoukariApril 12, 2016

Da yammacin ranar Litinin ce (11.04.2016) aka sanar da sabuwar majalisar ministocin Kasar Nijar da ta kumshi sabi da kuma tsofin ministoci 38 ba tare da 'yan adawa ba.

https://p.dw.com/p/1ITbM
Niger Amtseid des neu gewählten Präsidenten Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Nijar Issoufou MahamadouHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Tsohon minista a fadar shugaban kasa kuma shugaban jam'iyya mai mulki Bazoum Mohamed ya samu mukamin ministan cikin gida, yayin da tsohon ministan cikin gidan Hassoumi Massaoudou ya zama ministan tsaro. Foumakoye Gado ya sake dawowa a kan mukaminsa na ministan man fetir, yayin da shi ma Seidou Sidibe ya sake dawowa kan mukaminsa na ministan kudi, sai kuma Aishatou Boulama da a baya ta rike ofishin ministan hakokin waje, ta zamo ministan fasali kuma dukanninsu daga jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya. Sai dai an damka ofishin ministan harkokin waje a halin yanzu ga Ibrahim Yacoubou shugaban sabuwar jam'iyyar nan ta Kishin Kasa da ya zo na biyar a zagaye na farko na zaben shugaban kasar wanda a baya jam'iyyar mai mulki ta koreshi daga cikin ta a lokacin da yake a matsayin daraktan fadar shugaban kasa.

Ministan yada labarai Yahouza Sadissou Madobi ya koma ministan sadarwa da ya kumshi dukkannin fannin wayoyin sadarwa da gidan waya na aike wa da wasiku, yayin da tsohon dan majalisa Assoumana Malam Issa na jam'iyya mai mulki ke a matsayin kakakin gwamnati kuma ministan raya al'adu. Ministan Shari'a Marou Amadou ya sake samun tsohon mukaminsa, inda Abouba Albade shugaban sabuwar jam'iyyar Jamhuriya ya zama ministan kula da harkokin noma da kiwo.