Nijar ta gano masu kulla makarkashiyar hari kan bututun mai
June 22, 2024Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, ta tabbatar da gano makarkashiyar da ake kulla mata game da tunkuda man fetur dinta cikin bututun da ke bi ta Jamhuriyar Benin, biyo bayan ikirarin da wasu tsageru suka yi na cewa su suka kai harin, a wani mataki na bukatar sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Karin bayani:Nijar ta dakatar da tunkuda man fetur dinta zuwa Jamhuriyar Benin
Gidan talabijin din kasar Tele Sahel, ya rawaito gwamnan Zinder Kanar Issoufou Labo da ya kai ziyara wurin da aka kai harin, na cewa sun kammala tattara bayanan sirri kan wadanda suka kitsa harin bututun man, kuma za su kama su domin tuhumarsu da laifin ta'addanci.
Karin bayani:Kasar Benin ta kama wasu 'yan Jamhuriyar Nijar
A ranar 12 ga watan Yunin nan da muke ciki ne dai 'yan ta'adda suka kai hari a karon farko kan jami'an tsaron da ke kula da bututun man, inda suka kashe sojojin Nijar 6.