Nijar ta katse alaka da kungiyar kasashen rainon Faransa OIF
December 25, 2023Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun sanar da katse alaka da kungiyar kasashen rainon Faransa OIF, a kokarin kasar na yanke duk wata hulda da uwargijiyarta da ta yi ma ta mulkin mallaka Faransa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Karin bayani:Nijar: Ko alaka da Faransa ta zo karshe?
A wani jawabi da mai magana da yawun gwamnatin Kanar Amadou Abdramane ya gabatar a gidan talabijin din kasar, ya ce Faransa tana amfani da kungiyar ta OIF mai mambobi 88 domin ci gaba da kare muradanta, inda Nijar din ke kira ga sauran kasashen Afirka da su dukufa wajen yada harsunansu, don fitar da kai daga tunanin da masu mulkin mallaka suka kakaba musu.
Karin bayani:Nijar: Iyalan Bazoum sun maka talabijin RTN a kotu
Wata sanarwa kuma ta daban da sojojin suka fitar, ta ce har yanzu ba su yanke iya adadin lokacin da za su kwashe a kan karagar mulkin ba kafin mayar da shi hannun farar hula, face sai an kammala sauraron taron kasa na jin ra'ayin jama'a.