1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta soke kawancen tsaro da EU

Abdul-raheem Hassan
December 5, 2023

Gwamnatin mulkin soji a Nijar, ta soke kawancen sojanta da kungiyar Tarayyar Turai EU, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar cewa ta janye izinin wani shirin EU da aka kakulla don ƙarfafa rundunar tsaro a kasar.

https://p.dw.com/p/4ZmEe
Shugaban mulkin soji a Nijar, Abdourahamane TchianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

A shekarar 2012 ne aka kaddamar da tawagar farar hula ta EUCAP Sahel a Nijar, don taimakawa jami'an tsaron kasar yaki da 'yan bindiga da sauran kungiyoyin ta'adda da ke wa kasar barazana da sauran kasashen yankin Sahel, inda aka tura kusan turawa 120 na dindindin zuwa sansanin.

Gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta karbi mulki a watan Yulin shekarar 2023, kuma gwamnatin ta tilasta sojojin kasar Faransa da ke taimakawa yaki da ta'addanci ficewa daga cikin kasar.