Nijar ta ce a fitar da jakadan Faransa daga kasar
August 31, 2023Sanarwar ta birnin Yamai ta ce an soke dukkanin takardun diflomasiyyar da kuma Visarsa da na iyalansa. A baya dai, gwamnatin sojin kasar da ta hambarar da Mohamed Bazoum daga mulki ta bai wa Sylvain Itte sa'o'i 48 da ya fice daga kasar a makon da ya gabata. Sai dai Faransa ba ta yi wa jakadan nata kiranye ba bayan da wa'adin ya cika a ranar 28 ga watan Agusta.
Karin bayani: Sojojin Nijar sun kori karin wasu jakadu daga kasar
Cikin wata sabuwar sanarwa da Faransa ta bayar a wannan Alhamis, ta jadadda cewar har yanzu tana kan bakarta na cewar jakadanta zai ci gaba da aiki a Yamai saboda ba ta amince da sojojin a matsayin jagoroin Nijar na halak da malak ba. Dangantaka dai na kara yin tsami tsakanin Jamhuriyar Nijar din da kuma uwargijiyarta Faransa.
Karin bayani: Sabuwar baraka tsakanin Nijar da Faransa