Zargin Faransa a Jamhuriyar Nijar
October 4, 2023Talla
Da yammacin jiya Talata Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine na Jamhurtiyar Nijar, ya gana da kungiyoyin Maluman adinai, yan kungiyoyin fararan hula, da na sarakunan gargajiya, inda ya sanar da su halin da ake ciki a kasar dangane da zargin cewa kasar Faransa na kitsawa da zimmar wargaza kasar ta Nijar ta sabili da cewa sabin hukumomin na mulkin soja sun nemi da sojojin Faransa dubu uku da dari biyar (3500) sun fice daga kasar wanda hakan bai yi wa kasar ta Faransa dadi ba.