1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar tana bikin tuna ranar kafa tafarkin dimokradiya

July 29, 2014

A jamhuriyar Nijar shekaru ukku kenan da gwamnati ta kaddamar da wannan rana domin tunawa da ranar da aka bude babban taron mahawara na kasar ran 29 ga watan Yuni na shekara ta 1991. turbar demokrasiyya.

https://p.dw.com/p/1Cm2c
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou IssoufouHoto: DW/M. Kanta

Albarkacin wannan rana ta yau wacce ta zo a daidai
loakcin da ake fama da danbarwar siyasa a kasar, gwamnatin kasar tare
da hadin guywar kungiyoyin farar hula sun shirya babban taron mahawara
inda aka yi bitar tafiyar democrasiyyar kasar ta Nijar.


Wakillai 200.000 ne wadanda su ka fito daga kungiyoyin
kwadago da na dalibbai da na yan siyasa da dai sauran rukunnan al'umma
su ka halarci babban taron mahawara na kasa wato Conf Nationale wanda
aka share watanni ukku da kwana 8 ana yi daga ranar 29 ga watan Yulin
shekara ta 1991. Wannan taro ne dai ya kai ga dora kasar ta Nijar akan
turbar democradiyya da fara da mulkin rukon kwarya da kuma zaben
Alhaji Mahaman Usmane shugaban jamiyyar CDS Rahama jagoran kawancan
jamiyyu masu ra'ayin sauyi a matsayin zabebben shugaban kasar Nijar na
farko. A bikin tunawa da wannan rana a bana, masana da wasu yan mazan jiya
da su ka halarcin taron na Conf Nationale sun shirya bababn taron
mahawara, inda su ka yi nazarin yanayin da democrasiyyar Nijar din
shekaru 23 bayan girkuwarta a kasar. Malam Nuhu Arzika na kawancan
kungiyoyin farar hula na MPCR, daya daga cikin wadanda su ka gabatar da
lacca a gurin taron ya yi bayani a game da matsalolin da ke hana ruwa
gudu ga democrasiyyar kasar ta Niger:

"Yan siyasa a yau su mu ke kuka da su domin su duk abun da ya damesu
shine kaka za su yi a zabe su, kuma bayan an zabe su sun samu iko
kokowar da su ke ita ce yaya za a yi su ci zaben gaba su kuma wadanda
ke adawa tunaninsu shine kaka za mu yi mu gurguntar da milki dan an yi
maza maza a koma zabe. In an zabe mu batun milkin mi nene ya kamata mu
yi shi wanann ba a zancan shi.,Kuma a yau a cikin jam'iyyun siyasa su
kansu ba bu zancan democradiyya a cikinsu, domin milkin kama karya da
danniya da yaya zan samu kudi shi ke a gabansu. Ta kai duk wanda ya
samu gaba tunaninsa shine yaya zai yi ya samu kudi, ya mamaye sauran ya
dannesu. Kuma yau mutanemmu talauci da fatara sun sanya basa tunanin
mutuncinsu kawai neman kare cikinsu su ke, alhali duk mutumin da ya
sanya cikinsa a gaba ba ya tunanin mutuncinsa, to wannan shi da dabba
ba su da nisa."

Shima dai daga nasa bangare Mallam Yakuba Magaji, wakillin kungiyar
dalibban Nijar a taron mahawarar na kasa, kuma shugaban wata kungiyar
farar hula mai suna APPD Kirikiri zargin yan siyasar kasar ta Nijar
ya yi da kasancewa ummulhaba'isan koma bayan da democradiyyar kasar ta
ke fuskanta:

"In kuka yi lissafi cikin shekarunnan 23 juyin milki hudu aka yi saboda
rikicin yan siyasa bisa kan munahuci da makirci da rashin duba goben
Niger. Sai wanann yan adawa su game kai da sojawa su yi ma yan majority
juyin milki. Dan ku ga lokacin Mahaman Usmane haka aka yi yan siyasa su
ka kulle masa ita sai da aka yi masa juyin milki, haka zalika Baare
Mainasa da Tanja Mammadu, kuma wadannann yan siyasa namu yan siyasa ne
wadanda kamar ana ganin za su dau darasin jiya ko shekaranjiya, amma hakan bai samu ba. Ka ga kenan ba a kai labari da wadannan yan siyasa, kenan ya zamo
tilas sai an nemi mutane democratte na kirki a je gaba."

Babu dai wani babban dan siyasa na bangaran adawa ko majority da ya
bukaci mayar da martani akan zargin da ake yi masu.To Amma Parpesa
Tijjani Alu masanin ilimin kimiyyar siyasa, kana mashawarci ga
shugababn kasa cewa ya yi akwai alkahiran da deocrasiyyar ta samar ga
kasar.

Niger Tuareg Friedensforum
Taron zaman lafiya tsakanin gwamnati da AbzinawaHoto: Bettina Rühl
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Alamar dimokradiya: Majalisar dokokin NijarHoto: DW

"Mun yi zama wani lokacin da in ka bada ra'ayinka kana iya sanya ranka
cikin hadari amma ka gani da democrasiyya kana iya bada labari abbu
wani tsoro. Kuma a fannin siyasa akwai jam'iyyu da dama kuma ko wace
na neman milki ba bu wata matsala, kuma yau ikon zuwa ne ka ke ka
bayyana raayinka ga al'umma in sun amince su zabe ka kuma in sun zabe ka
ba dan ka tsaya akan milki ba ne har illa masha Allahu. To ka ga ko ai
wanann ci gaba ne sosai."

Daga karshe dai kungiyoyin, tare da hadin guywar gwamnatin sun bada
shawarar shirya irin wanann taro na bitar tafiyar democrasiyyar kasar
ta Nijar lokaci zuwa lokaci a tsawon shekara da zummar bayyanawa ko
wani rukunin al'umma irin laifukansa, dama neman ra'ayoyinsu akan
hanyoyin karfafa tafarkin democradiyyar kasar ta Nijar.

Mawallafi: Gazali Abdou Tassawa
Edita: Umaru Aliyu