1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Yaki da cutar zazzabin cizon sauro

Salissou BoukariAugust 5, 2016

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar kungiyar UNICEF sun ayyana yaki da cutar zazzabin cizon sauro da kuma tamowa don kare yara kanana.

https://p.dw.com/p/1JcHg

Wannan rigakafin ana yin shi ne a jihohi bakwai daga cikin jihohi takwas na kasar musamman ma a wannan lokaci na damuna inda aka fi samun yaduwar sauron da ke haddasa wannan cuta da ke daya daga cikin manyan cutukan da suka fi saurin kisa a kasashe masu tasowa.

Akalla dai za a kashe kudaden da suka kai miliyan dubu hudu da rabi na CFA cikin wannan aiki na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro da kuma tamowa, inda mutane fiye da 9000 za su yi wannan aiki a sassa daban-daban na kasar har ya zuwa Jihar Diffa mai fama da matsalar Boko Haram. Wani hade-haden magungunnna ne dai ake bai wa yaran a matsayin na riga kafin kamuwa da cutar ta zazzabin cizon sauro.