1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojoji na yi wa 'yan uwan Bazoum bita da kulli

Abdourahamane Hassane
December 1, 2023

Iyalan hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum sun ce ba su ji duriyarsa ba tun ranar 18 ga watan Oktoba, sun kuma yi tir da kame da bincike na cin zarafi da ake yi wa wasu daga cikin danginsu.

https://p.dw.com/p/4ZhAH
 Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A cikin wata sanarwa da suka fitar wada kamfanin dilancin labaran na Faransa AFP ya bayyana Iyalen tsohon shugaban sun ce ba su da labarinsa da maidakinsa da kuma dansa wanda ak tsare da su a fadar gwamnatin. Sannan sun ce da yawa daga cikin iyalansu na fuskantar kamu da kuma bincike daga hukumomin sojoji. A ranar Lahadin da ta gabata, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun yi awan gaba  Ali Bey Mahjoub, wani babban jami'in banki kuma kawun Bazoum. Yayin da da ranar tara ga watan Nuwamba, sanarwar iyalan ta ce an cafke. Ali Mabrouk, basaraken gargajiya kuma ɗan'uwan matar Bazoum, a kudancin damgaram